Akidojin ImamiyyaDa yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan Akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, Ja’iri, mai wauta, mai wasa, makaryaci, mai yaudara, da yake aikata mummunan aiki yana barin kyakkyawa, Allah ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa[17]. Kuma Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayiâ€. Surar Mumin: 23. “Kuma Allah ba ya son barnaâ€. Surar Bakara: 31 “Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu muna Masu wasa baâ€. Surar Dukhan: 205. “Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta miniâ€. Surar Zariyat: 56. Da sauran ayoyi masu girma, tsarki ya tabbata gareka ba ka halicci wannan don barna -rashin manufa- ba. 9- Hawan Hukunci A Kan Baligi Mun yi imani cewa Allah (S.W.T) ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani. Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a.
|