Akidojin ImamiyyaKuma ni ina mai wasiyya ga ‘yan’uwana masu karatu da cewa kada damar karanta wannan addu’a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tunani a kan ma’anoninta da abubuwan da take nufi tare da halarto da zuciya da fuskantowa zuwa ga Allah da tsoro da kaskan da kai, da kuma karanta ta tamkar yana magana da kansa ne, tare kuma da bin ladubban da aka ambata daga Ahlul Baiti (A.S) Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to maganar baka ce kawai kuma ba ya kara wa mutum sani, ba ya sama masa kusanci, kuma ba ta yaye masa bakin ciki kuma ba a amsa masa addu’a da shi. “Hakika Allah mai girma da buwaya ba ya karbar addu’a daga zuciya rafkananniya, don haka idan ka yi addu’a ka fuskanto da zuciyarka sannan ka ji cewa lalle za a amsaâ€[39]. 35- Addu’o’in Sahifatus Sajjadiyya Bayan aukuwar al’amarin karbala mai ban takaici da kuma kame ragamar shugabancin al’ummar musulmi da Banu Umayya suka yi kuma suka dulmuya a cikin danniya suka yi dumu-dumu da jinin mutane sa’an nan suka yi watsi da koyar war Addini, sai Imam Zainul Abidin (AS) wato Sayyiddus Sajidin Ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici, yana gida babu wani mai kusatarsa kuma ba zai iya yada wa mutane abin da ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba. Sai ya tilastu a kan ya dauki salon addu’a wanda muka ambata da cewa yana daga cikin hanyoyin tsarkake zukata a matsayin hanyar yada koyarwar Alkur’ani da ladubban Musulunci da kuma sanar da tafarkin Ahlul Baiti (AS) kuma hanyar cusa wa mutane ruhin Addini da zuhudu da abin da ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi’u. Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar wa mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da ke matsa masa ba, kuma ba zasu iya kafa masa wata hujja ba, don haka ne ya yawaita yin wadannan addu’o’i masu zurfi, a an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya wanda ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammad (S.A.W). Salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, da kuma mafi daukakar addini, da mafi ingancin asiran tauhidi da Annabci da kuma mafi ingancin hanyar koyar da kyawawan dabi’u ababan yabo da kuma ladubban Musulunci. Kuma ta kunshi maudu’ai daban daban ne na tarbiyya ta Addini da ta shafi koyarwar Addini da kyawawan dabi’u ta hanyar addu’a, ko kuma addu’a ce amma da salon koyar da Addini da kuma kyawawan dabi’u. Shi ne salon bayanin Larabci mafifici kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u bayan Alkur’ani da Littafin Nahjul Balagha. Daga cikinsu akwai wanda yake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, da yabonsa da gode masa da komawa zuwa gareshi. Daga ciki akwai wadda ke sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah da kebewa da shi da sirrinka da yankewa zuwa gareshi, daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma’anar Salati ga Annabi (S.A.W) da Manzannin Allah da zababbunsa daga cikin halittunSa da yadda ake yin sa, daga cikinsu akwai wadanda zasu fahimtar da kai abin da ya dace ka bi iyayenka da shi, da kuma abin da zai yi maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa da na da a kan mahaifinsa, ko kuma hakkokin makwabta, ko na dangi ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka. Daga cikin addu’o’in akwai wanda zai fadakar da kai kan abin da ya wajaba na basussukan mutane akan ka, da kuma abin da ya kamata ka sani na al’amuran tattalin arziki da dukiya, a abin da ya kamata ka yi mu’amala da shi ga abokanka da sauran mutane baki daya, da wadanda kake neman yin mu’mala da su a maslaharka, da kuma abin da zai hada maka dukkan kyawawan dabi’u, kuma ya zama maka tafarki cikakke na ilimin kyawawan dabi’u. Daga cikinsu akwai wadanda zasu koya maka yadda za ka yi hakuri a kan munanan abubuwa da suke aukuwa da kuma yadda za ka yi yayin da kake ciwo da kuma yayin da kake kalau. Daga cikinsu akwai wadanda ke maka sharhin ayyukan wajibi da suka hau kan sojojin Musulunci da wajiban mutane dangane da su, da dai sauran wadannan da kyawawan dabi’u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu’a. Abubuwan da suke kunshe cikin addu’ar imam su ne: Na farko: Sanin Allah da girman kudurarSa da bayanin kadaita Shi da tsarkake shi da mafi zurfin kalmomi na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu’a da salo mabambanta, kamar yayin da kake karantawa a addu’a ta farko: “Godiya ta tabbata ga Allah na farko wanda babu wani na farko da ya kasance kafin shi, na karshen da babu wani na karshe da zai kasance bayansa, wanda idanuwan masu gani suka gaza ganin sa, wahamce-wahamcen masu sifantawa suka gajiya wajen siffanta Shi, Ya fari halittu da kudurarSa a farkon farawa ya kuma kago su kamar yadda ya so kagowa.â€. Karanta ma’anar na farko da na karshe da kyau da kuma tsarkake Allah (S.W.T) daga kasancewar wani gani ko wahami ya gewaye da shi, da kuma tunani kan zurfin ma’anar halittawa da samarwa.
|