Akidojin ImamiyyaTayar da Matattu ba wani abu ba ne sai dawo da mutum ranar tashin kiyama da jikinsa bayan rididdigewa da sake dawo da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge. Ba wajibi ba ne a yi imani da dalla-dallan tayar da Matattu fiye da abin da Alkur’ani ya ambata ko sama da abin da ya fada na daga; Hisabi da Siradi da Auna ayyuka da Aljana da Wuta da Sakamako da Ukuba daidai gwarbwadon abin da bayaninsa ya zo a cikin Kur’ani mai girma. “Bai wajaba ba sanin hakikar da babu mai iya kaiwa gare ta sai ma’abocin zurfin ilimi, kamar ilimin cewa shin Matattu zasu dawo ne da kan kansu ko wasu makamantansu ne? Kuma shin rayuka zasu rasu ne kamar jiki ko kuwa zasu ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jiki yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanci mutum ne ko ya hada har da dukan dabbobi ne? Kuma shin tashin a lokaci daya ne ko a sannu-sannu ne? Kuma idan yin imani da Aljanna da Wuta wajibi ne amma bai zama dole a san cewa samammu ne a halin yanzu ba, ko kuma sanin cewa a sama suke ko a kasa ko kuma sun saba. Haka nan idan sanin ma’auni ya zama wajibi amma bai wajiba ba a san cewa ma’aunin na ma’ana ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu. Kuma ba dole ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri ko kuwa daidaituwa a kan tafarki madaidaici ne. Hadafi wannan bayani shi ne a Musulunci ba a shardanta bincike domin sanin cewa wadannan abubuwa suna da jiki ne ko kuwa…â€[57]. Wannan akidar ta tashin kiyamar da saukin nan nata ita ce wacce Musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya wuce haka domin saninta dalla-dalla sama da abin da Kura’ani ya zo da ita domin ya gamsar da kansa don kore shakkun da masu bincike da masu kokwanto ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali ko bahasin dalili na zahiri to yana wahalar da kansa ne kuma zai fada a cikin mushkiloli da jayayya maras iyaka. A Addini babu adinda yake tilasta wannan zurfafawar dalla-dalla da littattafan masana Akida da malaman falsafa suke cike da shi, kuma babu wata larurar Addini ko ta zamantakewa ko siyasa da take tilasta irin wadannan rubuce-rubucen da makalolin da aka makale littattafai da ita babu wata fa’ida, wadanda suka karar da karfi da kokari da lokuta da tunanin masu jayaya ba tare da fa’ida ba. Gamsuwarmu game da gazawar mutum game da riskar wadannan al’amuran da suke boyayyu a gare mu, kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu, sun wadatar wajen raddin wadannan shubuhohi da shakkun da ake tayarwa game da wadancan bayanai. Tare da sanin cewa Allah (S.W.T) mai iko ne a kan ya ba mu labarin hakikanin aukuwar Tashin kiyama da tashi daga kabari. Ilimin dan Adam da gwaje-gwajensa da bincike-bincikensa mustahili ne su iya samo wani abu da bai san shi ba, ba ya kuma karkashin gwajinsa da bincikensa da ba zai iya saninsa ba sai bayan mutuwarsa da ciratarsa daga wannan duniya zuwa wata duniyar daban, idan haka ne yaya za a saurari ya yi huknci da tabbatarwa ko kore wannan abu balle ya shiga bayanansa dalla-dalla da abubuwan da suka kebanta da shi, sai dai idan ya dogara a kan bokanci da zato da mamaki kamar yadda yake a dabi’ar dan Adam ya yi mamakin dukkan abin da bai saba da shi ba, kuma iliminsa da riskarsa ba su san shi ba, kamar mai fada da jahilcinsa yana mai mamakin tashi daga kabari da tashin kiyama: “Wanene zai rayar da kasusuwa alhali suna rididdigagguâ€. Ba komai ne ya sa shi mamakin ba sai rashin sabawa da ganin matacce rididdigaggen an mayar masa da sabuwar rayuwa, sai dai mai wannan mamakin ya manta da yanda aka halicce shi tun farko alhalin da can ya kasance rasasshe, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu an hada su ne daga kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma sarari da abin ya tattaro har ya zama mutum madaidaici mai hankali: “Shin mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya buga mana misali ya mance halittarsaâ€. Ana gaya wa mai irin wannan maganar da ya mance kansa: “Wannan da ya fare ta tun karo na farko shi ne zai raya ta kuma shi masani ne game da dukan halittaâ€. Kuma a ce masa: Gashi bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa kuma ka san Manzo da abin da ya ba da labari game da shi, da gajiyawar iliminka hatta a gano sirrin halittarka da sirrin samuwarka, da yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon mani da ba ya jin komai ba ya hankalta zuwa marhalolin da ke biye da aka harhada daga kwayoyin halitta manesanta, domin ka zamanto mutum madaidaici mai hankali mai tunani mai riska da mariskai. Kuma a ce da shi: Yaya kake mamakin dawo maka da rayuwa sabuwa bayan ka zama rididdigagge, kana kokarin tsinkayar sanin abin da kwarewarka ka da iliminka ba zasu iya gano shi ba? A kuma ce masa: Ba ka da wata mafita sai mika wuya kana mai ikrari da wannan hakika wadda mai juya al’amuran halittu, masani, mai kudura, wanda ya samar da kai daga rashi. Kuma dukkan wani kokari na binciko abin da ba zai yiwu a gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne maras amfani, da rudani cikn dimuwa, da bude ido a cikin duhu mai dudum. Dan Adam duk da irin inda ya kai gare shi na ilimi a wannan zamani, ya kago lantarki, da rada[58], da amfani da makamin kare dangi, da sauran kage-kagen da, da an yi magana game da su a shekarun baya da an kirga su a cikin mustahilan abubuwa ababan yi wa isgili, amma duk da haka mutum ya kasa gano hakikanin wutar lantarki, da sirrin kwayar zarra, ya kasa gano hatta hakikanin daya daga cikin siffofinta, to yaya zai ji kwadayin gano sirrin halitta da samuwa, sannan ya kara gaba yana son ya san sirrin Tashin kiyama da Tashi daga kabari. Haka ne, ya kamata ga mutum bayan ya yi imani da Musulunci ya nisanci bin son zuciya kuma ya shagaltu da abin da zai gyara masa lahirarsa da duniyarsa, da kuma abin da zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abin da zai taimake shi a kansa da kuma abin da zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan halarta a gaban mai Mulki mai yawan sani. “Kuma ku ji tsoron ranar da wata rai ba ta wadatar wa wata rai komai kuma ba a karbar ceto daga gareta kuma ba a karbar fansa daga gareta kuma ba a taimakon suâ€. Bakara: 48. GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI
|