Akidojin ImamiyyaAmma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan Addini suna daga kyawawan ayyuka a shari’a wannan al’amari ne da ya tabbata a fikihu, ba nan ne wajan tabbatar da shi ba. Abin da muke so mu yi bayani a nan shi ne; gudanar da irin wadannan ayyuka ba ya daga cikin irin nau’o’in shirka da Allah kamar yadda wasu suke rayawa, ba kuma bautar imamai ba ne, sai dai abin da ake nufi shi ne raya al’amuransu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “wannan, duk wanda Ya girmama alamomin Addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukataâ€. Surar Hajj: 32. 7- Siffofin Ubangiji (S.W.T) Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa akwai siffofi tabbatattu na hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi, da iko, da wadata, da irada -nufi-, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne da suke kari a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala. Na’am siffofinsa sun sassaba a ma’anoninsu ne ba a hakikaninsu da samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi. Tabbatattun siffofi na idafa[11] kuwa, kamar halittawa, da arzutawa, da gabatuwa, da kuma samarwa, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da kuma la’akari daban-daban. Amma siffofin da ake kira salbiyya -korarru- wadanda ake kiransu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore kasancewarsa mai yiwuwar samuwa[12] ba wajibin samuwa ba, abin da yake nufin kore jiki, da sura, da sura, da motsi, da rashin motsi, da nauyi, da rashin nauyi, da makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa. Sannan kuma kore kasancewarsa ba wajibin samuwa ba yana tabbatar da kasancewarsa wajibin samuwa, wajabcin samuwa kuwa yana daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah (S.W.T) kuwa Makadaici ne ta kowace fuska, babu yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawa a hakikaninsa makadaici sidif. Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra’ayin cewa siffofi tabbatttu suna komawa ne zuwa ga siffofi salbiyya, saboda ya kasa gane cewa siffofin Allah su ne ainihin zatinsa, sai ya yi tsammanin cewa siffofi tabbatattu suna komawa zuwa korewa ne domin ya samu nutsuwar imani da kadaitakar zati da rashin kididdigarsa, amma sai ya fada cikin abin da yake mafi muni saboda sanya ainihin zati wanda shi ne ainihin samuwa, kuma tsantsar samuwa wanda ba shi da wata nakasa ko wata fuska ta siffar yiwuwar samuwa. Sai ya sanya shi ya zama aininin rashi kuma tsantsar korarre[13], Allah ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma zamewar duga-dugai. Kamar yadda mamaki ba ya karewa ga wanda yake da ra’ayin cewa siffofinSa na subutiyya -tabbatattu- kari ne a kan zatinSa, ya yi imani da kididdigar zatin Allah wajibin samuwa, da samuwar ababan tarayya[14] gareshi, ko kuma wannan magana tasa ta kai shi ga imani da hauhawar zatinsa madaukakin sarki. Shugabanmu Amirul Muminin (A.S) ya ce:
|