Akidojin Imamiyya



 

24- Ismar Imami

Mun yi Imani da cewa wajibi ga Imami ya zama katangagge daga dukkan munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da gangan ko da rafkanwa kamar yadda annabi yake. Haka nan wajibi ne ya zama katangagge daga rafkanwa da kuskure da mantuwa, domin Imamai su ne masu kare shari’a, masu tsayar da ita, halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin kuwa da ya hukunta mana imani da ismar annabawa shi ne ainihin dalilin da ya hukunta mana imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci ba.

Ba wani abu ba ne a wajan Allah

Ya sanya duniya a abu daya

 

25- Siffofin Imami

Mun yi imani cewa imami kamar yadda annabi yake, wajibi ne shi ma ya zama mafificin mutane a siffofin kamala, kamar jaruntaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al’amura, da hankali da hikima da kuma kyawon dabi’a, dalilinmu na wannan siffofi ga Annabi shi ne dalilinmu na siffantuwar wadannan siffofi ga imami.

Amma game da iliminsa kuwa, shi yana samun ilmi da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukan saninsa ta gurin Annabi ne ko kuma Imamin da ya gabace shi, Idan kuma aka sami wani sabon abu to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhama da karfin kwakwalwar da Allah ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al’amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure, kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka ko koyarwar malamai, duk da yake iliminsa yana iya karuwa, shi ya sa Annabi (S.A.W) a addu’arsa yake cewa: “Ubangiji ka kara mini ilmi”[33].

Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayyar dan Adam cewa kowane mutum yana da wata sa’a ayyananniya ko wasu awowi a rayuwarsa da yakan san wani abu da kansa ta hanyar kaifin fahimta wanda shi a kan kansa reshe ne na ilhami, saboda abin da Allah ya sanya masa na karfin yin haka. Wannan karfi yana sassabawa da sabawar mutane a karfinsa da rauninsa da yawansa da karancinsa. Sai kwakwalwar mutum ta kai ga sani da ilmi ba tare da ya bukaci wani tunani ba da kuma kawo mukaddima da hujjoji na hankali ko kuma koyawar malamai ba, kuma saudayawa mutum kan sami irin haka a kan kansa a rayuwarsa, Idan kuwa al’amarin haka yake to ya halatta mutum ya kai ga kololuwar daraja da kamala a karfin tunaninsa na sanin ilhami, wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da da na yanzu suka tabbatar da shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next