Akidojin ImamiyyaTa yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da Addininsu kafin su yi bincike game da ingancin shari’ar da ta biyo bayansu, kamar Kiristanci dangane da Yahudanci ko musulunci dangane da Kiristanci da Yahudanci. Wajibi ne a bisa hukuncin hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga bayansu, idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta su bar Addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su wanzu a kan Addininsu na da, su kuma karkata zuwa gareshi Amma musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci to ba ya bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci Addininsa da kuma wadanda ake da’awa bayansa. Wadanda suka gabata dai domin shi ya yi imani da su, to don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da su, sai dai kawai ya yi hukunci da cewa ita shafaffiya ce da Shari’ar Musulunci don haka bai wajaba ya yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littattafansu ba. Amma wadanda ake da’awarsu daga baya kuwa dalili shi ne saboda Annabin Musulunci Muhammad (S.A.W) ya ce: “Babu wani Annabi bayanaâ€. Kuma shi mai gaskiya ne kuma Amintacce. “Kuma shi ba ya magana a kan son rai, ba wani abu ba ne face wahayi da aka yi masaâ€. Surar Najmi: 3-4. Don haka saboda menene zai bukaci dalili a kan ingancin da’awar Annabcin da aka yi da’awarsa daga baya ba idan har mai da’awar ya yi da’awa. Na’am yana wajaba a kan musulmi -ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da ma’abocin sako (S.A.W) da kuma sabanin mazhabobi da ra’ayoyi da samuwar kungiyoyi- ya yi bincike Ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce-hukuncen da aka saukar shari’a kamar yadda suka zo. Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari’ar da aka saukar kamar yadda take alhali musulmi sun sassaba, jama’a jama’a sun rarraba, babu salla guda daya, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai iri daya ba a cikin dukkan mu’amala... don haka yaya zai yi? ta wace irin hanya zai yi salla? da wane ra’ayi zai yi aikin ibada da mu’amalarsa kamar aure, da saki, da gado, da saye da sayarwa, da tsayar da haddi, da daiyya da sauransu? Kuma bai halatta gare shi ya bi ra’ayin iyaye ba ko ya koma ga abin da zuriyarsa da mutanensa ke kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah (S.W.T) domin a nan babu wata alkunya ko sassauci ko bangaranci. Na’am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da ke kansa tsakaninsa da Allah ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai zarge shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawaiâ€. Surar Alkiyama: 36. “Lalle shi mutum a game da kansa mai gani neâ€. Surar AlKiyama: 14. “Lalle wannan fadakarwa ce ga wanda ya don haka ga wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsaâ€. Surar Muzzammil 19. Farkon abin da mutum zai tambaya shi ne; shin ya kama tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Baiti (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya Isna Ashara masu bin Imamai sha biyu shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori daban daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi, daga cikin Mazhabobi hudun ne ko kuma daga wasu Mazhabobin daban da suka rushe? Haka nan tambayar zai ta ta zo wa wanda yake da ‘yanci a tunani da zabi, har sai ya kai ga wani ga gaskiya a bar dogaro. Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bincike a kan abin da ke biye da ita a akidar Imamiyya Isna Ashariyya. FASALI NA UKU
|