Akidojin Imamiyya15 Azar 1382 H.SH 6 Disemba 2003 M 1-Sani Kan Samuwar Allah Mun yi imanin cewa saboda baiwar da Allah ya yi mana ta karfin tunani da kuma kyautar hankali, to ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Za mu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya neâ€. Surar Fussilat: 53 Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai baâ€. (Surar Bakara: 170) Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zatoâ€. Surar An’am: 116 A hakika mu abin da muke yin imani da shi shi ne cewa: Hankulanmu su ne suke wajabta mana yin tuntuntuni kan halittu da sanin mahallicin duniya, kamar yadda suke wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da’awar annabta da kuma mu’uijzarsa. Kuma bai inganta ba -a hankalce- a yi koyi da wani a cikin wadannan al’amuran komai matsayinsa da darajarsa.
|