Akidojin ImamiyyaSai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema? Na ce: Na’am. Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai? Na ce: Na’am. Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin. Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi? Ya ce: Na’am. Abbana ya ce: Sai na tafi, bayan nan –wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kale ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba? Na ce: Haka ne! Ya ce: “Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
|