Akidojin ImamiyyaKarfin ilhama a gun imami ana cewa da ita “kuwwa kudsiyya†wato karfi daga Allah, da take mafi kamalar kololuwar darajar ilhama, sai mai wannan siffa a kowane lokaci a kuma kowane hali ya so ya san wani abu sai ya san shi ba tare da mukaddima ba ko koyarwar wani malami, sai ya koma wa wannan abin domin saninsa sai ya san shi tare da taimakon wannan karfi da Allah ya ba shi, sai ilimi da wannan abu ya bayyana gareshi tamkar yadda bayyanar surar abu take bayyana a tsafatataccen madubi. Wannan kuwa abu ne bayyananne a tarihim Imamai (A.S), su a wannan fage kamar Annabi suke ba su taba yin tarbiyya ko neman ilmi a hannnu kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwanu shekarun balaga, karatu ne ko kuwa rubutu, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu duk kuwa da cewa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa Kuma ba a taba tambayar su wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar (ban sani ba) daga bakinsu ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu, alhali kuwa ba za ka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba sai ka ji an ambaci wanda ya tabiyyatar da shi ya koyar da shi, da kuma wadanda ya karbi ruywaya ko ilimi a hannunsu, da kuma dakatawarsu a wasu mas’aloli ko kokwantosu a mafi yawa daga ilimomi kamar yadda yake a kowane zamani da kowane guri. 26- Biyayya Ga Imamai Mun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul’amri†Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarkin zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar ilminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa kamar yadda Taurarin suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W). A wani hadisin yana fada: “Misalinsu a cikin wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa ba sa rigonsa da magana kuma su da umarnninsa masu aiki neâ€. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa. Mu mun mun yi imani da cewa umarninsu umarnin Allah ne, haninsu hanin Allah ne, biyayya gare su biyayya ce gare shi, saba musu kuma saba Masa ne, kuma Soyayya gare su soyayya ce gare shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi, bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne. kuma ya wajaba a mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu. Saboda haka mun yi imani da cewa hukunce-hukuncen Shari’ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta ba sai daga garesu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun nutsuwa da cewa ya bayar da wajibin da aka dora masa sai ta hanyarsu. Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S) ne duk wanda ya hau ya tsira wanda kuwa ya jinkirta ya bar su ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makale da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da’awowi da jayayya. Bahasin imamanci game da tabbatar da cewa su ne halifofi na shari’a kuma masu shugabanci da izinin Allah a wannan zamanin ba shi ne muhimmi ba, wannan al’amari ne na tarihi da ya wuce, kuma tabbatar da shi ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari’a ba. Abin da yake muhimmi shi ne abin da muka ambata na wajabcin komawa zuwa garesu wajan karbar hukunce-hukuncen shari’a, da kuma sanin abin da manzo (S.A.W) ya zo da shi kamar yadda ya zo da shi ta fuska ingantacciya.
|