Akidojin ImamiyyaAbu Ja’afar (AS): To Babu komai kenan. Sa’id: To halaka ke nan. Abu Ja’afar (AS): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna. 3- Muhawar Imam Sadik (A.S) da Abu Sabah Al’kinani[47]. Al’kinani: Muna shan wahalar mutane game da ku. Abu Abdullah: Mene ne abin da kuke gamuwa da shi daga mutane?. Al’Kinani: Magana ba ta gushewa tsakaninmu da mutun, sai ya ce: Wannan Dan Ja’afariyya ne mugu. Abu Abdullahi: Mutane suna aibata ku da ni?. Al’kinani: E. Abu Abdullah: Wallahi karancin mai bin Ja’afar a cikinku ya yawaita! Kadai sahabbaina shi ne wanda tsantseninsa ya tsananta, ya yi aiki don mahaliccinsa ya kaunaci ladansa, wadannan su ne sahabbaina!
|