Halayen Zamantakewa (A.S)



Fahimtar Kur’ani

a-Komawa zuwa ga Ahlil Baiti (A.S) a tafsirin kur’ani mai girma da fahimtar hakikanin addinin musulunci daga gareshi, wannan kuma ta hanyar sanin mai shafewa da wanda aka shafe, da muhkam da mutashabihi, da khas da amm, da mujmal da mubayyan, da kuma dalilan saukar aya, da makamancin haka yana daga abin da yake da alaka da fahimtar kura’ni da sharhinsa da tafsirinsa. Hakika musulmi sun hadu a kan cewa Ali (A.S) da ahlin gidansa (A.S) su ne suka fi kowa sanin kur’ani daga waninsu na daga malaman msusulunci, kuma nassosi da dama daga littattafan jama’a biyu (sunna da Shi’a) sun yi nuni da haka:

Hakika ya zo daga gareshi (A.S) ya ce: “Yaya zaku maye ni game da al’amarin sakalaini, aka ce: menene sakalaini ya manzon Allah? Ya ce: mafi girma shi ne littafin Allah tsani ne da gefensa ya ke hannun Allah, gefe kuma a hannunku sai ku yi riko da shi ba zaku taba zamewa ba ko ku bata, karamin shi ne zuriyata domin su ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske ni a tafki, na tambayi ubangijina game da su, kada ku shiga gabansu sai ku halaka kada ku sanar da su domin su sun fi ku sani[16]â€‌.

Sanin Sunna

b-Komawa zuwa ga Ahlul Baiti wajan sanin sunnar Annabi, wannan kuwa domin ita sunnar ta samu matsaloli da kuma gurbatawa da shiga duhu, sakamkon aikin nakali da karbo hadisi da tafsiri wanda ba amintacce ba, da kuma tazara tsakanin nassin hadisi da yanayin yadda ya zo, da kuma dalilan kago hadisai da kirkirar su da karya ga manzon Allah (S.A.W), ko kuma sakamakon ijtihadi da sandarar da nassi da rashin riko da shi da nuna cewa akawai maslaha da tilasta da suka sanya wannan barin nasa da kuma daina amfani da nassin hadisin. Al’amarin da ya kai ga cakudawa da rudarwa da rashin nutsuwa wajan fahimtar shari’ar musulunci.

Hakika mabiya Ahlul Baiti (A.S) sun bambanta da wannan a aikace a kan waninsa na daga musulmi da komawarsu su kadai[17] wajan riko da sunna da kuma sharhinta da fahimtarta da sanin mai shafewa da shafaffe, da sakakke da mai kebancewa, da kebantacce da gama-gari, kamar yadda mabiya Ahlul Baiti (A.S) suke kudurcewa cewa Ahlul baiti (A.S) sun kiyaye sunnar Annabi gaba daya ba tare da bukata zuwa ga komawa zuwa ga dalilai na zato ba domin isa zuwa ga hukuncin shari’a.

Taklidi Da Mujtahidi Adili Rayayye

C-Kiyaye wa da ma’auni a aikin riko da hukuncin shari’a a iyakokin mujtahidi adili da mutane suke sane da shi da ijtihadi, da adalci, da takawa, da tsentseni, ta hanyar bincike da kuma jin daukar nauyi game da shi, ba ta hanyar bayar da izinin hakan ga wannan mujtahidi ta hannun mahukumta ko dagitai ba.

Komawa zuwa ga mujtahidi a fatawa ko hukunci da kuma iyakance matsayin shari’a a hukunci da husuma, da lizitar fatawar mujtahidi rayayye[18] da yake rayuwa da wadannan mas’aloli da sukan faru ta wata nahiya, kuma zai yiwu ga mtane su san abubuwan da suka kebanta da shi da kuma siffofinsa ta wata nahiya.

Wannan al’amura sun sanya bayar da dama ga mabiya Ahlul Baiti (A.S) su kasance sun motsa a cikin bayanin shari’a, ba tare sun bujiro ga matsaloli na fatawa da sauran jama’ar musulmi suka fuskanta ba, ta yadda ta kai su ga tanakudi da sabani mai girma har zuwa ga jayayya a fatawa da hukunci da daukar matakai. Ta yiwu wannan shi ne sirrin da ya sanya Annabi (S.A.W) ya karfafa muhimmancin komawa Ahlul Baiti (A.S) a hukunce-hukuncen shari’a, da muhimmantar da wilaya da biyayya da halifanci, ta yadda ya zo daga Annabi (S.A.W) a mutawitarin magana da karfafa wa a kan haka kamar yadda abin da hadisin sakalaini ya kunsa: “Cewa ni bar muku sakalaini littafin Allah da itrata ahlin gidana matukar kun yi riko da su ba zaku taba bata ba bayana har abada, kuma ba zasu rabu ba har sai sun riske ni a tafki[19]â€‌.

Haka nan karfafawar Ahlul Baiti (A.S) ga wadannan abin komawa zuwa garesu ta zo a hadisai bayyanannu masu yawa, ta yadda suka tarbiyyatar da shi’arsu a kan lizimtar hakan, suka kuma tsoratar da su daga fadawa cikin karkacewa ko dogara da zato da istihsani wajan sanin hukuncin shari’a.

3-Siffantuwa Da Daraja Madaukakiya Ta Kamalar Mutuntaka

Wannan siffa, bayan kasancewarta hadafi na msusulunci ga mutum musulmi, ta na kuma nuna mana mahangar Ahlul Baiti (A.S) ga sharadi na dole da ba makawa ga wannan jama’a ta gari da ta siffantu da shi domin ta zama zata iya tsayuwa da aikinta muhimmi a tarihin dan Adam, ta yadda wannan daraja madaukakiya zata zama mai iko a kan tasiri a tarihin dan Adam, da kuma neman saukar da alhairai da albarkatai na ubangiji a kan al’umma: “Da cewa mutanen alkarya sun yi imani sun ji tsoron Allah da mun bude masu albarakatai daga sama da kasa sai dai sun karyata, sai muka rike su da abin da suka kasance suna aikatawa[20]â€‌.

Saboda haka ne muka samu cewa Ahlil Baiti (A.S) suna karfafa wannan siffa ba a matsayin tarbiyyatar da shi’arsu ba kawai, sai dai ya hada har da bayanin matsayin yanayin wadannan Shi’a da samuwarsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next