Halayen Zamantakewa (A.S)



 

Samuwa Mai Kamala Mai Karfi

Samar da zamantakewa mai karfi ga wannan jama’a kuma mai dogaro da kai a ruhinta da ma’ana maras dogara da tsari da dawagitai suke tilasawa a al’ummar musulmi, haka nan mai nisanta daga tasirin yanayin zamantakewa gurbatacciya, da kuma dogara a kan haka, a kan karfafawa da neman taimkon ubangiji da dogaro da kai ga wannan jama’a tagari.

Zai yiwu mu yi la’akari da wannan a cikin tarihin musulunci ta hanyar wasu alamomi da, da sannu zamu yi magana game da su kamar yadda zai zo a wannan bahasi:

a-Tsarin siyasa da yake misaltuwa a tsarin jagorancin malami, da hukunci da fatawa, ta yadda mujtahidai zasu dauki wannan nauyin a wannan tsari da imaman Ahlul Baiti (A.S) suka shirya shi ga shi’arsu, hakika imamai sun tsayar da tsari mai zurfi da ya dace da tsarin siyasa na gama-gari na gaba daya na al’umma da kuma kiyayewa ga jama’a ta gari wajen dogaro da kanta a lokaci guda, da kuma ikonta da karfinta a kan tsayuwa da muhimmin aiki da ake bukata, da rashin saraya da faduwa daga yanayin siyasa lalatacce da kuma komawa zuwa ga mahukunta da kuma kai hukunci wajan dagutu. Da sannu zamu yi magana game da wannna tsari in Allah ya so.

Tsarin dukiya ga jama’a wanda yake samar da abubuwan yi yau da gobe na masrufin ayyukan addini na gaba daya a wannan tsakatsaki, wanda ya dogara daga asasi a kan hakkokin shari’a wanda zakka da khumusi su ne gaba a wannan fage, ta yadda wannan tsari ya zama yana da rawa mai girma da ya taka wajan kare jama’a ta gari a cigabanta. Wannan kuma abu ne wanda da sannu zamu bincike shi a tsarin tattalin arziki na jama’a.

Samuwar mu’assasai na wayarwa da tarbiyyatarwa kamar makarantu da hauzozi na ilimi da da suka yaye mujtahidai da ma’abota kwarewa a ilimin shari’a da dama, wacce ta zama Katanga mai karfi wajan tarbiyyatar da al’umma da kare ta daga daidaicewa. Hakika Ahlul Baiti (A.S) sun karfafa a kan wajabcin neman ilimi da kuma larurar bayar da ilimi daga bangaren malamai.

Daga Amirul muminin (A.S) yana cewa: “Ya ku mutane, ku sani kamalar addini shi ne neman ilimi da aiki da shi. Ku sani neman ilimi ya fi neman kudi zama wajibi. Hakika dukiya an raba shi kuma an lamunce wa kowannenku, kuma mai adalci tsakaninku shi ne ya raba shi ya lamunce maku shi kuma zai cika muku alkawari, amma ilimi abin taskacewa gun ma’abotansa ne, kuma hakika an umarce ku da nemansa daga ma’abotansa ku neme shiâ€‌[44].

Kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi cewa “Neman ilimi wajibi neâ€‌, “Ku sani Allah yana sn msau neman ilimiâ€‌, “Kuma wanda ya kama hanyar neman ilimi kamar mai yaki ne a tafarkin Allahâ€‌.

An rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa ya ce: “Ku yi muzakara ku yi haduwa ku bayar da hadisi hakika hadisi yana yaye hasken zuciya, kuma zukata suna yin tsatsa kamar yadda takobi take yin tsatsa, hadisi shi ne yake yaye taâ€‌.

Hakanan samar da majlisosi da tarurruka da ake ambaton falalolin Ahlul Baiti (A.S) da kuma gadonsu na ilimi da wayewa da kyawawan dabi’u da sha’anin rayuwa na yau da kullum na jama’a. haka nan abin da zamu samu na janibin wayewa.

Himmantuwa da samar da kudi ga jama’a ta gari ta hanyar cinikayya da noma, wadanda suke samar da wani abu na tsari na tattalin arziki yana mai nisanta daga tasirin dagutai da dokokinsu da kuma ayyukansu da kuma korar su ga mutane da sa musu takunkumi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next