Halayen Zamantakewa (A.S)



Daga wannan ne zamu samu cewa imamai (A.S) suna kasa imani a kan siffofin da mumini yake siffantuwa da su, suna ganin taklifi yana wajaba ya zama daidai gwargwadon iyawar mutum.

Daga Ammar dan Al’ahwas, daga Abu Abdullahi Sadik (A.S) ya ce: “Hakika madaukaki ya sanya imani rabo bakwai, a kan biyayya, da gaskiya, da yakini, da yarda, da cika alkawari, da ilimi, da hakuri, sannan sai ya raba wannan tsakanin mutane, wanda aka sanya masa kashi bakwai shi ne cikakke mai juriya, aka bayar da wasu kashin ga wasu sashen mutane, wasu kuma rabo biyu, wasu kuma uku, har suka tuke zuwa kaso bakwai. Sannan sai ya ce: Kada ku dora wa mai rabo daya aikin mai rabo biyu, ko mai rabo biyu uku, sai ku rusa su, sai ya fadi haka har sai da ya kai ga mai rabo bakwaiâ€‌[64].

Daga Sudair a hadisi ingantacce ya ce: “Abu Ja’afar albakir ya ce da ni: Hakika muminai suna kan matsayansu ne, wasu a kan daya, wasu a kan biyu, wasu a kan uku, wasu a kan hudu, wasu a kan biyar, wasu a kan shida, wasu kan bakwai, da ka dora wa mai daya biyu ba zai iya ba, ko mai biyu ka dora masa uku ba zai iya ba, ko mai uku hudu ba zai iya ba, ko mai hudu biyar ba zai iya ba, ko mai biyar shida ba zai iya ba, ko mai shida bakwai ba zai iya ba, hakan nan wannan darajoji sukeâ€‌[65].

Da haka ne imanin mutum ya zama abin yi wa gargadi yayin da yake karkata daga barin kykkyawan aiki da barin kyawawan dabi’u, haka nan imani yake karuwa yana cika ta hanyar lizimtar ayyuka na kyawawan dabi’u.

Kamar yadda wannna yake bude mana hanyar tarbiyya da tafiyar da al’amauran mutane, duk sadda imanin mutum ya fi karfi da kamala ya fi cancanta ga daraja madaukakiya na daukar nauyi da yake kansa, kuma dukk sadda imaninsa ya zama yafi karanci to ba makawa a kiyaye shi a kuma iyakance masa ayyuka kamar yadda ruwaya da ta rigaya ta yi bayani.

Ba makawa wannan fahimta ga imani da kuma muhimmancin kyawawan dabi’u a cikinsa, yana da tasiri mai girma da kuma al’amari mai kyau a kan lizimtar wannan hali da kyawawan dabi’u, da kuma daukar nauyi mai girma da al’amura masu nauyi.

Jagoranci Da Kyawawan Dabi’u

4-Karfafawa a kan sahabbansu da mabiyansu da su yi riko da misalta jagoranci cikin al’ummar musulmi da kuma tsakanin daidaikun jama’ar musulmi, da kuma aiki domin kai wa ga saduwa zuwa misali mafi girma da daukaka cikin jama’a, ta yadda wadannan mutane zasu zama amintattu da samun nutsuwa da su tsakanin daidaikun jama’ar musulmi.

Ba makawa cewa dabi’u kyawawa da nagarta da lizimtar aikin da ya dace da su, su ne zasu iya kai wa ga bayar da wannan al’amari da ake bukata cikin al’ummar musulmi.

A cikin hikimar tarihi da kur’ani yake magana akai yana nuna nau’i biyu na jagoranci da koyi.

Na farko: Nau’in kyau (jagoranci na gari), wannda shi ne koyi mai kyau da ya tsayu a kan nagarta da lizimtar kyawawan dabi’u, kamar koyi da Ibrahim (A.S) da wadanda suke tare da shi, da Muhammad (S.A.W) da annabawa da manzanni (A.S). Ubangiji madaukaki ya ce: “Lallai koyi ya tabbata gareku da manzon Allah ga wanda yake kaunar ranar lahira ya kuma tuna Allah dayawaâ€‌[66]. Madaukaki ya ce: “Hakika koyi ya tabbata gareku ga Ibrahim da wadanda suke tare da shi yayin da suka ce wa mutanensu mu mun barranta daga gareku da kuma abin da kuke bautawa sabanin Allahâ€‌[67].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next