Halayen Zamantakewa (A.S)



 Alhalin zamu ga wasu jama’ar musulmi sun fuskanci komawa zuwa ga malamai daban-daban da suke lizimtuwa da wata akida da fikira sananniya, sai ya zama Ba’ash’are ko Bamu’utazile ko Mufawwadi ko makamantansu na daga akidoji da saudayawa mutum kan iya sabawa da malamin da yake bi a fikihu a bangaren nazari na akida da fikira.

Saboda haka ba zaka samu malamai da mujtahidai na Shi’a da mabiyansu a kan irin wannan sabani na akida da fikira da muke gani cikin malaman sauran mazhabobin musulmi ba.

Gamammiyar Akida

3-Gamewa a mazhar akida, ta yadda Ahlul Baiti (A.S) suka taba kowane abu da ya shafi akida da sharhi da bayani dalla-dalla sai ya zama ya shafi komai na dukkan mas’alolin akida, ba su bar wani fage ba na wannan janibi a hannun mujtahidai da ra’ayoyinsu ba ko ijtihdinsu da fitar da hukucinsu.

Wannan kuwa ya zama haka ne saboda mas’alar akida ta na da hadari kwarai kuma sakamko mai muni zai iya kasancewa idan aka samu kuskure a cikinta, kuma wannan kuskuren idan ya faru zai bayyana a dukkan gini na asasin tunani da na zamantakewa da siyasa da cigaban rayuwa na â€کyan adamtaka.

Don haka ne zamu ga cewa Ahlul Baiti (A.S) ba su takaita ba wajan yin magana kan janibin akida da usul dinta a kan assin akida ta msusulunci kamar tauhidi da annabta da tashin kiyama kawai, sai dai ya shafi dukkan fage daban-daban kamar adalci, imamanci, da tilasci, da zabi, da kaddara, da Kafirci da imani da alakarsu da aiki, da isma, da adalci, da mutuwa, da rayuwa, da sunnonin tarihi, da jarrabawa, da wilaya, da so, da ki, da kyaywawan dabi’u, da bayyanar mahadi (A.S) a karshen zamani, da alamomin alkiyama, kamar barzahu, da tashin kaburburwa da daidaita su, da tafkin annabi, da siradi, da ganin Allah da hisabi, da ceto, da aljanna da wuta, da azaba da hutu, da dawwama a wuta da aljanna, da kyakkywa da mummuna, da wahayin ubangiji, da hankali.

Wannan bayani dalla-dalla da makamantansu da imamai suka yi suka kuma yi maganin da kuma warware matsalar janibin tunani da akida, suka ba ta matsayi mai karfi wanda yake da matsayi mai girma a karfin ka’idar akida, da kuma karfafa ginin jama’a ta gari da kuma daidaita sahunta.

Zai iya yiwuwa mu ga wannan gamewa idan muka komawa littafin Aka’idus saduk da sharhinsa na shaihul Mufid, da ya dogara tun asali bisa bayanai dalla-dalla a kan ruwayoyin da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S).

Tayiwu mafi girma dalili a kan muhimmancin wannan aiki na assasa wannan ka’ida zamu ga lokacin rayuwar imamai (A.S) ya samu sabani mai yawa a tsakanin mabiya ahlul bait (A.S) saboda rassan da wadannan akidu suka yi, sai dai yayin da imamai (A.S) suka samu damar tabbatar da fadadawa a game da bayanin akida sai ga tanakudi da sabani da yake cikin wadancan sassabawa ya karanta zuwa sosai a wannan zamani na gaiba babba, tare da cewa lokacin gaiba yafi lokutan rayuwar imamai wahala sakamakon gaiba da rashin damar ikon haduwa da su, wannan kuma bai kasance ba sai saboda wannan aikin babba da imamai suka yi tsayi a kansa a lokacin samuwarsu, da kuma lamuncewa ta samar da akida da fikira ga wannan jama’a saliha. Kamar yadda tarihin musulunci ya shaida da sabani na akida mai fadi bai kuma gushe ba tsakanin al’ummar musulmi sakamakon rashin ittifakinsu a kan makoma daya bayan kur’ani mai girma, ta yadda zata zama makoma ga musulmi gaba daya, kai babi ma wannan sam.

Kur’ani mai girma duk da ya kasance abin da duka aka hadu a kansa sai dai shi yana karbar tawili, saboda haka ne ma imamai (A.S) suka karfafa muhimmancin samuwar mai fassara kur’ani, haka nan kuma Annabi (S.A.W) ya karfafa muhimmancin daya nauyin da yake su ne Ahlul Baiti (A.S) a hadisin sakalaini da hadisin safina[53].

â€کYancin Tunani Da Kuma Hankali Kubutacce

4-kafa ka’idoji ingantattu a wajan warware mas’alolin tunani da akida, wannan kuma ta hanyar karfafa â€کyancin tunani da akida a al’ummar musulmi, da ta tsayu a kan asasin:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next