Halayen Zamantakewa (A.S)



Madaukaki ya ce: “Koyi kyakkyawa ya tabbata gareku a cikinsu ga wanda yake kaunar Allah da ranar lahiraâ€‌[68].

 Madaukaki ya ce: “Wadannan su ne wadanda muka zo musu da littafi da hukunci da annabta, idan wadannan suka kafirce da su hakika mun wakilta wasu mutane da su ba ma su kafirce wa ba ne da su. Wadannan su ne wadanda Allah ya shiryar, da shiriyarsu ne zaka yi koyiâ€‌[69].

Na biyu: Mummunan jagoranci da koyi, wadannan su ne wadanda suke kafuwa bisa asasin karfi da iko da nuna mamaya a fili, kuma su ne jagorancin jabberanci da dagutanci, kuma shugabanni munana ma’abota fuska da dukiya.

Allah yana cewa: “A’aha! sun ce ne mu mun sami iyayenmu a kan wani al’amari kuma mu masu shiryuwa ne bisa tafarkinsuâ€‌[70]. Madaukaki ya ce: “Suka ce ya ubagijinmu mu mun bi shugabanninmu da manyanmu ne sai suka batar da mu tafarkiâ€‌[71].

Ta yadda mutum yake zama bisa al’ada karkashin tasirin dayan wadannan abubuwa biyu na asasi a al’amarin koyi da jagoranci wadanda su ne: Al’amarin fidira kubutacciya, da madogarar gaskiya da adalci, da ji na badini, da kuma son rai, da sha’awa, da tsoro, da kwadayi, da kuma rauni, da jin tawayar rai.

Hakika Ahlul Baiti (A.S) sun kwadaitar da mabiyansu a kan al’amari na farko da kuma amfana daga gareshi domin kaiwa zuwa ga al’amarin jagorancin zamantakewar al’umma da jama’a.

Daga Abdillahi dan Abu Ya’afur daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: “Ku kasance masu kiran mutane da alheri ba da harshenku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga garekuâ€‌[72].

Daga littafin majalis daga dan abbas ya ce: “An ce ya manzon Allah!: Wane abokin zama ne ya fi? Sai ya ce: “Wanda ganinsa yake tuna muku Allah, maganarsa take kara muku ilimi, aikinsa yake kwadaitar da ku lahiraâ€‌[73].

Daga Imam Zainul abiding (A.S): “Mafi munin mutane a wajan Allah madaukaki shi ne wanda ya yi koyi da sunnar imami amma ba ya aiki da ayyukansaâ€‌[74].

Adalci Da Kyawawan Dabi’u

5-An bawa adalci[75] muhimmanci mai girma a rayuwar zamantakewar al’umma mai tsari, ta yadda aka shardanta samuwar siffar adalci a mazhabar Ahlul Baiti (A.S) ga mutane da suke daukar nauyin ayyuka da dama kamar: shugabanni, da jagorori, da alkalai, da masu fatawa, da limaman sallar jam’i, da shaidu a husuma, da shaidun saki, da waninsu na daga wajaje daban-daban da mai bin littattafan fikihu zai iya samunsu. Al’amari da yake nuna muhimmancin da aka ba wa wadannan siffofi da kuma muhimmancinsu, har adalci ya zama yana da muhimmancin da aka gabatar da shi a kan ilimi, da sani, ta yadda babi wata kima ga malami ba tare da aiki da takawa ba, kai malami yana iya juyawa ya koma wani abu mai cutarwa idan babi takawa, saboda haka gargadi mai tsanani ya zo daga imaman Ahlul Baiti (A.S) daga malamai miyagu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next