Halayen Zamantakewa (A.S)



a-Magana ta hankali da kuma karfafa hankali da ji na badini da fidirar mutum tsarkakakkiya.

b-Lizimtuwa da marja’ancin kur’ani mai girma da nassin Annabi ingantacce, yana mai nisanta daga son rai da kuma siyasa ta musamman, da kuma nisanta daga amfani da shu’uri da ji da karkata na al’ada da zato na kashin kai na danadamtaka da kuskure ya yawaita a cikinsa, kamar kiyasi da istihsani, abin da Ahlul Baiti (A.S) da Annabi (S.A.W) suka ambace shi da da “ra’ayiâ€‌ da hadisai sun zo da magana game da shi, misali: “Wanda ya fassara kur’ani da ra’ayinsa hakika ya kafirtaâ€‌ da hadisin “Hakika addini ba a riskarsa da hankulaâ€‌[54].

Hakika karfafawa ta zo game da karfafa komawa ga kur’ani sake-ba-kaidi da sunna ingantacciya a ruwayoyi masu yawa daga cikinsu ruwaya daga Ayyuba dan Hurr ya ce: “Na ji Abu Abdillahi (A.S) yana cewa: Duk wani abu abin komarwa ne zuwa littafin Allah da sunna, duk wani hadisi da ba ya daidai da littafin Allah shi batacce neâ€‌[55].

Daga gareshi (A.S) ya ce: “Duk abin da ya zo muku daga hadisi ba ya gaskata littafin Allah to shi bata neâ€‌[56].

c-Bude kofar ijtihadi da fitar da hukuncin shari’a a cikin ka’idoji da usulai ingantattu, da kuma aiki a kan bayanin kur’ani a kan dukkan al’amari da suke fuskantar dan Adam daga asali kuma budadde ga dukkan abin da ake tsammanin da yanayi da mutum zai iya fuskanta.

Wannan â€کyanci na tunani ya kasance, haka ma wannan lizimtuwa da ka’idoji da iyakokin musulunci na fitar da hukunci (nassin kur’ani da sunnar Annabi), wannan budewar tunani da sabuntuwa a fahimta da kuma nazari a wajan warware mas’aloli, wannan dacewa tare da duk abin da ta ke bukata na fidirar mutum da hankali da ji na samuwa yana daga kebantattun siffofi da karantarwar Ahlul Baiti (A.S) ta kebanta da shi da kuma wannan jama’a saliha kamar yadda muka yi nuni.

Wannan yana daga hususiyya da wannan jama’a ta gari ta kebanta da shi wajan tsayuwa da nauyin da yake kanta wajan kare akidar musulunci da fikirar musulunci ta asali, ba kawai a wajan fuskantar fikira da akida da take samammiya a cikin al’ummar musulmi da kewayen musulunci ba kawai, har ma da fuskantar tunaninnika da akidu da suke wajan da’irar musulunci gaba daya.

Bangaren Kyawawan Dabi’u

Kyawawan dabi’u ne ya ke zuwa martaba ta biyu wajan muhimmancin gina al’umma, ta yadda ya zama shi ne ya ke misalta asasi na biyu wanda gina al’umma ya ke wajaba ya kasance a kansa, kuma shi ne yake nuna janibin samuwa ta badini da ma’ana a ayyukan mutum da alakar mutumtaka wacce ta ke damfare da maganar adalci da zalunci, da kyau da muni, da kamala da saraya zuwa ga tabewa ta ruhi, da a kan tafarkin rayuwar dan Adam. Wanda malaman falsafa suke cewa da shi akalul amali (hankalin da ake auna aiki da shi) da yake sabanin akalun nazari wanda janibin akida da fikira yake dogara da shi kamar yadda muka yi nuni.

Zai iya yiwuwa mu yi la’akari a cikin wannan bahasi game da gina jama’a ta gari da wadannan bayanai masu zuwa:

Muhimmancin Kyawawan dabi’u A Tsarin Hukuncin Shari’a

1-Karafafawa ga matsayin kyawawan dabi’u a tsari da hukuncin shari’a na al’umma, da kuma alakarta da nufi da irada na dan Adam da kamalarta ta hanyar daukar nauyi dangane da ita, ta yadda wadannan bangarori biyu suka zama mafarar sabani mai zurfi a akidar musulunci. Da yawa daga masu tunani na msulumi suka tafi a kan akidar tilastawa, wanda take nufin mutum ba shi ne yake daukar nauyin hakikanin mas’uliyyar da take kansa ba dangane da karkacewa a tafarki da kyawawan dabi’u da kuma raba wannan da iradarsa, shi a nan mai kasakanta ne da dukkan samurawarsa ga iradar Allah da ayyukansa wadanda suke ainihin ayyukan Allah ne da halittarsa, a wannan akida zamu iya ganin babi wata ma’ana a kaddara azabatar da mutum a kan sabawarsa ga hukuncin shari’a wanda wannan ya saba wa adalcin Allah, ko kuma mu ce abu ne mummuna a kan Allah ya aikata hakan, wannan kuma saboda mutum yana da mariskai na kyawawan dabi’u masu zaman kansu da suke nuna masa yin hukunci da mummuna, ko kyakkyawa, kawai yana kansa ne ya lizmci hukuncin shari’a domin hukuncin shari’a umarni ne na Allah da nufinsa, kuma mutum halitta ne na Allah, haka ma dukkan sha’aninsa, Allah kuma ba a tambayar sa game da wannan al’amari “Ba a tambayarsa game da abin da da yake aikatawa amma su ana tambayarsuâ€‌.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next