Halayen Zamantakewa (A.S)



Shiryawa Domin Bayyanar Mahadi (A.S)

Hakika dukkan addinan sama wanda musulunci daga cikin su sun yi bishara da bayyanar mai gyara mai tseratarwa a karshen zamani da karshen tarihin danAdam “domin ya cika duniya da daidaito da adalci bayan an cikata da zalunci da ketare iyakaâ€‌.

Wannan tunani ya zo da albishir mai karfafawa ga hakikar da take cikin kur’ani wanda take karfafawa a kan gadon jama’a saliha da aka raunatar a bayan kasa ga duniya: “Hakika mun rubuta a littafi bayan ambato cewa kasa bayina ne nagari zasu gaje ta[7]â€‌. Allah ya yi alkawari ga wadanda suka yi imani daga cikinku suka kuma yi aiki na gari zai sanya su masu halifanci a bayan kasa kamar yadda ya sanya wadanda suka gabacesu zai kuma tabbatar musu addinin da ya yardar musu zai kuma canzamusu aminci bayan tsoro su bauta mini kada su yi shirka da ni da wani abu[8]â€‌.

Kamar yadda wannan ya dace da wata hakika da kur’ani mai girma ya yi nuni da ita na rinjayen gaskiya a kan bata a dukkan dauki-ba-dadi da yake faruwa a tarihin dan Adam, wanda yake nufin al’marin tarihi ta hanyar taimakon Allah da sa hannunsa ga aiko manzanni da saukar da littattafan sama da kuma al’marin kamala ba makawa daga karshe ta kai ga zuwa ga kamalar danAdam da annabawa da salihai suka yi albishir da shi.

Hakika sakon karshe (na musulunci) ya zo yana mai bayanin cikar danAdam a waccan marhalar a matsayin wayewa da riskar abin da yake faruwa na hakika, da kamar nazari domin tsayar rayuwar danAdam, da kuma cigaban kamala na alaka daban-daban a al’umma. Sai dai cewa kamala a matsayin dabbakawa da aiktawa a aikace da lizimtar aiki bai tabbata ba a aikace cikakke, domin wannna matsayi na kamala yana bukatar tsawon lokaci na wahlhalu da zogi da jarraba.

A nan ne muhimmancin Ahlul Baiti (A.S) da kuma jama’a ta gari wacce suka tarbiyyatar domin wannan aiki zai zo, domin share fage ga wannna marhala ta tarihi, da kuma bayyanar wannan mai tsamarwa mai gyara ga danAdamtaka.

Saudayawa Ahlul Baiti (A.S) sun kasance suna jefa wannan fikira ta zuwan imam mahadi (A.S) wanda ake sauraro da zai tsayu da al’amarin al’umma domin tseratar da â€کyan Adam daga zalunci da fasadi, har ma mafi yawa daga musulmi a zamuna daban-daban na rayuwar Ahlul Baiti (A.S) kai hatta da wasu mabiyansu sukan yi zaton kowane daya daga cikinsu a zamaninsa cewa shi ne imam mahadi (A.S).

Mu a nan ba muna so mu yi magana ba ne game da loko-loko da tasiri na akida da siyasa, wanda ya shafi wannan nazari na cigaba da tunanin bayyanar imam mahadi (A.S) da tafiyar da al’amarin halitta, domin wannan yana da nasa fage da zamu yi bincike game da shi, sai dai abin nufi shi ne nuni zuwa ga muhimmin aikin share fagen bayyanar.

Imamai a mahangarsu sun riga sun sanya wannan al’amari a zuciyarsu yayin gina jama’a ta gari da zata yi wannan aiki a lokacin boyuwar imam mahadi, ba kawai a matsayin akida da tunani ba kawai, har ma a matsayin aiki, kuma daya daga hadafofin samuwar wannan jama’a ta gari a wannann zamani na musamman shi ne shirya share fagen bayyanar.

Zai iya yiwuwa wannan ya bayyana a fili a cikin jama’a ta gari ta hanyar aiki da bayanai da za a yi la’akari da su masu zuwa:

1- Bayyana Fikira Ce Rayayyiya

Wanzuwar fikirar bayyana rayayyiya a tsakanin jama’ar musulmi tare da alaka ta hakika da wannan akida da jiran sauraron bayyyanar[9], da sanya shi shi’ari da aka jefa a tunanin musulmi da kuma siyasarsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next