Halayen Zamantakewa (A.S)



Adalci a cikin kwakwalwar mabiya Ahlul Baiti (A.S) ya zama yana da wani matsayi na musamman, da kuma tasiri mai zurfi a kan matsayinsu daga mujtahidai da alkalai da kuma wadanda suke da wasu ayyuka na siyasa da kuma aikin al’umma.

Wannan matsayi da fahimta ga aldalci ba zaka iya samunsa a wata mazhaba ba daga mazhabobin msusulmi, ko kuma a cikin wasu addinai don gane da ita ba, ta yadda sauran mazhabobi suka karbi limancin fasiki a sallar jam’i, da kuma shugabancinsa ga hukumci, da rangwame ga shaidu.

Ba makawa adalci yana da wata ma’ana mafi fadi daga ma’anar amintacce ko madogara, saboda haka ne ya dauki ma’ana mai fadi ta kyawawan dabi’u.

Kamar yadda adalci yake sharadi ga shaidu haka ma yana sassabawa a matsayinsa na dabi’a game da adalcin da ba makawa a same shi ga alkalai, da shugabanni, da masu fatawa, ta yadda ya zama wajibi ne a nau’i na biyu ya zama adalcin yana da matsayi mai girma daidai gwargwadon nau’in nauyin da mutum ya dauka da kuma zamantakewar al’umma da wannan matsyi ya hau kai.

Tsarin Tarbiyyar Rai

6-An sanya matakai da hanyoyi da dokoki domin isar da jama’a saliha zuwa ga tsarkake rai da kuma samun matsayi na kyawawan dabi’u.

Imamai ba su bar wa wannan tsari wata siffa ta gama-gari ba sai da suka kwadaitar da mabiyansu a kan kaiwa zuwa garita, suna kuma niman lizimtuwa da ita, kuma sun sanya wa wannan al’umma hanyoyi da zasu iya lizimta domin kaiwa zuwa ga wannan hadafi da cimma wannan manufa da matsayi na kyawawan dabi’u, wanda daga cikin wannan hanyoyi akwai tsarin tarbiyyar rai.

Tarbiyyar Rai (Jihadun nafs): Nazari Da Tsari

A-Nazari

Ba makawa a farko mu kawo nau’in ganin da musulcunci yake yi wa maudu’in tarbiyyar rai da nazarinsa, ta yada zamu iya nuni atakaice zuwa ga wannan al’amura masu zuwa:

Na farko: Rayuwar mutane rayuwa ce mikakkiya mai tsayi, ba ta takaita a kan rayuwar duniya ba, domin ita marhala ce gajeriya mai iyaka dangane da rayuwar mutane cikakkiya. Saboda haka ne aka sanya rayuwar duniya rayuwa ce ta jarrabwa da gwaji, kamar yadda wannan rayuwa saboda gajartarta rayuwa ce ta wasa da ado da alfahari. Amma rayuwa mai tsayi ta hakika ita ce rayuwar lahira da natija da sakamako suke tabbata a cikinta kuma ake auna ta da awon adalci da gaskiya.

Na biyu: Ma’aunin kamalar rayuwar mutum ita ce nafs din mutum ba rayuwar duniya ba ko jikin mutum, domin ita rai mai wanzuwa ce mai ci gaba amma jikin mutum yana karewa ya kuma lalace a halitta ya canja.

Saboda haka jihadin nafs kamala ce ga wannan nafs din ta dan Adam.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next