Halayen Zamantakewa (A.S)



Na uku: Ubangji da ya halicci mutum ya sanya masa hankali da ilimi da sani na Allah da shiriya da kuma asanin gaskiya da maslaha da barna a dunkule, kamar yadda Allah ya sanya sha’awa, da kawa, da ado, ga rayuwar duniya domin ya jarrabe shi ya gwada shi ta wata nahiya, domin kuma sha’awa ta kasance wani karfi mai motsa shi ta wani bangaren, wadannan alamomi ne guda biyu masu daurantar juna masu kishiyantar juna a rayuwar mutum.

Ya kuma ba shi iko a kan yin ayyuka da kuma sawwala abin da zai zo na nan gaba na rayuwarsa da kuma nau’i nau’i na wannan sawwalawa, sai iradar mutum ta zama ita ce abu na karshe da zai dauki mataki a rayuwar mutum da zabinsa ga wannan aiki ko wancan.

Duk sa’adda mutum ya sanya hankali shi ne mai shiryarwa ga nufinsa da zabinsa kuma mai mamayewa a kansa, to sai ya zama mai tafiya a tafarkin kamala, kuma duk sa’adda ya sanya son rai da sha’awa su ne masu mamaye nufinsa masu kuma fuskantar da rayuwarsa sai ya zama ya kama hanya zuwa ga faduwa da saraya.

A kashi na farko zamu ga hankali ne ya ke juya sha’awa, sai ta kama hanya zuwa ga tunkuda shi zuwa ga kamala, amma a na biyu sai mu ga sha’awa tana komawa wani karfi ne mai rusawa mai halakarwa ga mutum.

Na hudu: Ubangiji madaukaki da ludufinsa da rahamarsa da samuwarsa da hikimarsa da iliminsa ya aiko annabawa da littattafai da manzanci, ya kuma saukar da wahayi akansu da shiriya domin su shiryar da mutane zuwa ga gaskiya da dacewa yayin da al’amari ya rikice musu gaskiya da karya suka cakude masu, ko kuma yayin da yake dimuwa yake gajiyawa ga riskarsa da sanin maslaha da barna, domin maslahohi da barna a bayninta dalla-dalla ko kuma yayin da suka cakude tsakaninsu mutum ba shi da ikon saninta, sai wadannan annbawa da manzanni suka tsayu da isar da wannan sako na manzanci da tsarkake rai da kuma koyar da ita littafi da hikima, da hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba, da kuma shaida a kan ayyukansu da iliminsu.

Na biyar: Iradar dan Adam idan ta yi daida da shari’ar Allah da take cikin hukunce-hukunce da iyakokin shari’a sai ran mutum ta sami kamala, domin ita a yayin nan zata dabbaku da gaskiya da maslaha. Wannan kuma yana bukata daga mutum ya yi kokari wajan yakar son ransa da kuma mamaye sha’awarsa da kuma dabi’arsa domin ya sanya ta ta yi daidai da hukuncin shari’a.

A’aha jihadin nafs yana zama tare da yakar son rai da sha’awa a kan kansa da mutum yake aikatawa domin kamalarsa da take ita ce ma’aunin kamalar dan Adam, kamar yadda yake samun kamala a jikinsa ta hanyar wasa jiki da motsa jiki.

Musulunci ya sanya wani tsari na tarbiyyar rai domin dan Adam ya samu kamala ta wannan haryar. Wannan tsari yana da rukunai da asasi da salo na aiki, a nan zamu yi nuni zuwa ga wannan rukunoni da asasai da maudu’ai na gama-gari wadanda suke da alaka da salo na ilimi a dunkule amma bayani dalla-dalla sai mu bar shi zuwa ga wani fagen[76].

B-Tsari

Zai iya yiwuwa mu takaita wadannan rukunai na tsarin tafarkin musulunci da jihadin nafs cikin bayanai masu zuwa da zamu iya samun su a bahasosin tarbiyyar rai daga littattafan kyawawan dabi’u na hadisi da na bayanai game da ilimomi[77]:

Na farko: Karfafa alaka da Allah ta hanyar tsananin yakini da shi da kuma dogara a kansa, da kyautata zato gareshi, da ikhlasi a aiki da niyya, da so don Allah, da tsoro don shi, da kuma kaunarsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next