Halayen Zamantakewa (A.S)



Ta yiwu mafificin abin da wannan bayani zai yi mana nuni kansa ya kuma bambance mana bambanci tsakaninsu ta hanyar wannan nassi da Kulaini ya rawaito a Kafi ta hanya ingantatta daga Humrana dan A’ayun daga Abu Ja’afar Albakir (A.S) ya ce: “Imani shi ne abin da ya tabbata a zuci ya kuma kwarara zuwa ga Allah, aiki kuma ya gasgata shi da biyayya ga Allah da mika wuya ga al’amarinsa, musulunci shi ne abin da ya bayyana na zance da aiki, shi ne abin da jama’ar mutane suke a kansa gaba daya, da shi ne ake kare jini da kuma gado da halarcin aure da kuma haduwa wajan salla, da zakka, da azumi, da hajji, kuma da wannan ne suke fita daga Kafirci su shiga imani, musulunci bai hada da imani ba, amma imani ya hada da musulunci, su suna haduwa a magana da aiki, kamar yadda ka’aba ta kasance a cikin masallaci amma masallaci ba ya cikin ka’aba, haka nan imani yana gamewa da musulunci amma musulucni ba ya gamewa da imani.

Hakika Allah madaukaki ya ce: “Larabawan kauye suka ce mun yi imani, ka ce: Ba ku yi imani ba amma dai ku ce mun musulunta, har yanzu imani bai (wada) shiga zuciyarku ba tukunaâ€‌. Maganar Allah kuwa ita ce mafi gaskiyar magana. Sai na ce: Shin mumini yana da fifiko a kan musulmi na wani abu na daga falala, da hukunci, da haddi, da makamancin wannan? Sai ya ce: A nan suna matsayi daya ne, sai dai mumini yana da falala a kan musulmi a ayyukansu da kuma abin da suke kusantar Allah da shi. Sai na ce: Shin Allah bai ce “Wanda ya zo da kyakkyawa yana da goma misalintaâ€‌ ba? Amma kuma ka ce: Su ba su da bambanci a salla, da zakka, da azumi, da hajji tare da muminai?. Sai ya ce: Shin Allah bai ce: “Ana ninninka musu ninki mai yawaâ€‌ ba? Muminai su ne wadanda ake ninninka musu mai yawa, su ne suke da kyawawa ga kowace kyakkyawa da suka aikata ninki saba’in, wannan shi ne falalar mumini, kuma Allah yana dada masa daidai gwargwadon imaninsa da ninki mai yawa, kuma Allah yana aikata abin da ya so ga muminai na daga alheri. Sai na ce: Shin ba ka ganin yanzu wanda ya shiga musulunci ya shiga imani? Sai ya ce: A’a, sai dai shi an raba shi zuwa ga imani ya kuma fita daga Kafirci. Da sannu zan buga maka misali da zaka fahimci falalar imani a kan musulunci: Shin kana ganin da ka ga wani mutum a cikin masallaci, shin zaka shaida da ka ganshi cikin ka’aba? Sai na ce: A’a, bai halatta ba in yi haka. Sai ya ce: Da ka ga wani mutum a cikin ka’aba shin zaka shaida da ka gan shi a cikin masallaci mai alfarma? Sai na ce: Na’am, sa ya ce: Yaya haka ta kasance? Sai na ce: Domin shi ba zai yiwu ya shiga ka’aba ba sai ya shiga masallaci, sai ya ce: Ka yi daidai ka kuma kyautata, sannan ya ce: Haka nan imani da musulunci sukeâ€‌[61].

Imani Da Kuma Aiki

3-Yin imani da Allah makaukakin sarki yana misalta mafi muhimmanci siffa ta kyawawan dabi’u ta kamalar dan Adam a aikace da kuma fitar da shi daga halin akida tsantsa da lizimtar gina ruhi tsantsa zuwa ga aikata aiki da dabbaka shi, wannan shi ne ma’anar imani bisa asasinsa na hakika da kuma ainihin kamala mai martabobi da darajoji da take kamala ce da daukaka da ake samun su ta hanyar aiki.

Ta bayyana cewa wannan maudu’i yana daga maudu’ai masu tayar da jayayya da sabani a lokutan imamai (A.S) ta yadda wasu malamai kamar yadda muka yi nuni a baya suka tafi a kan ceewa babi bambanci tsakanin imanin annabawa da imanin Iblis, domin hakikanin imani a gunsu shi ne lizimtuwa da cewa Allah samamme ne, wannan kuma imma ya zama gaskiya ko kuma ya zama karya, sai dai annabawa sun saba da iblis a aiki ba a cikin lizimtar hakikanin wannan akida ba.

Amma mazhabar Ahlul Baiti (A.S) -da ta riga ta tarbiyyatar da mabiyanta- ya saba da wannan ra’ayi, a wajanta akwai sabani tsaknin imani da Allah gun masu imani da shi, da kuma imanin wadancan ababan buga misali da su kamar shedan, a wajansu imani yana da tasairi har ya kai ga wata iyaka mai girma, kuma yana da hawa da sauka ta hanyar aiki. Duk sa’adda bawa ya lizimci zuciya mai aiki ya kuma yi aiki, to darajar imaninsa tana hawa ne da kuma karfafa shi wannan imanin, da kuma tabbatar zuciyarsa da akidarsa ta wani bangare.

hakika Kulaini ya rawaito a littafin Kafi ta hanya ingantatta daga Jamil dan Darraj ya ce: “Na tambayi Abu Abdullah (A.S) game da imani sai ya ce: Shaidawa babi wani abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammad manzon Allah ne. Sai na ce: Shin wannan ba aiki ba ne? Sai ya ce: E. Sai na ce: To menene aiki da bambancinsa da imani? Sai ya ce: Imani ba ya tabbata a gare shi sai da aiki, aiki kuma daga gareshi yakeâ€‌[62].

Wasu nassosi suna bayanin wannan da ma’anoni daban-daban, daga cikinsu akwai wannan hadisin da Kulaini ya rawaito shi a littafin Kafi daga Hammad dan Amrun nasiibi ya ce: “Wani mutum ya tambayi Al’alim (A.S), sai ya ce: Ya al-alim, ba ni labari game da aikin da ya fi a wajan Allah?.

Sai yace: Abin da ba a karbar wani aiki sai da shi.

Sai ya ce: Menene wannan?.

Sai ya ce: Imani da Allah, wannan shi ne mafifincin ayyuka daraja, mafi daukakarta rabo, mafificinta matsayi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next