Halayen Zamantakewa (A.S)



A wata ruwaya daga Abu Ja’afar (A.S) ya ce: “Son mumini saboda Allah yana daga mafi girman rassan imani. Ku sani wanda ya so don Allah ya ki don Allah ya bayar don Allah ya hana don Allah to shi yana daga zababbun Allahâ€‌[33].

Kamar yadda bayan ya zo game da imani da addini da wannan ma’ana ta so, daga Fudail dan Yassar ya ce: “Na tambayi Abu Abdullah game da so da ki shin yana daga imani? Sai ya ce: Shin akwai wani imani in ba so ko ki ba?! Sannan ya karanta wannan aya: “Ya soyar da imani gareku ya kuma kawata shi a zukatanku ya kuma kiyar muku da Kafirci da fasikanci da sabo wadannan su ne shiryayyuâ€‌[34].

Daga Abu Ubaida Ziyad Alhazza daga Abu Ja’afar cewa shi ya ce: “Ya Ziyad, kaiconka shin akwai wani addini in ba so ba? Ba ka ganin fadin Allah madaukaki: “Ka ce in kun kasance kuna son Allah to ku bi ni Allah ya so ku ya kuma gafarta muku zunubbankuâ€‌[35].

Kamanta Jagoranci Kyakkyawa

Misalta koyi kyakkyawa tsakanin mutane a dabi’a ta daidaiku da kuma ta zamantakewar al’umma gaba daya: wannan tana daga siffa mafi muhimmanci da Ahlil Baiti (A.S) suka karfafa larurar siffantuwar Shi’a da ita, saboda haka ne suka sanya ta daya daga hadafofin gina al’umma ta gari kamar yadda muka sani tun farko.

Ta yiwu karfafa wa a kan siffantuwar Shi’a da siffar tsantseni da takawa da ikhlasi da ibada kamar yadda muka yi nuni akai tun farko yana misalta wani bangare daga bangarorin wannan siffa. Sai dai hada da wannan muna samun cewa Ahlil Baiti (A.S) suna karfafa wa shi’arsu himmantuwa da wannan siffofi da lizimtar karfafa wa da yake kamanta wannan koyi kyakkyawa cikin al’umma da kuma tsakanin mutane da la’akari da cewa wannan al’amri ne ma’bocin alaka ta musamman da aiki ingantacce da wannan jama’a ta gari zata gabatar a al’ummar musulmi, da kuma abin da zai iya yiwuwa ya zama yana da tasiri wajan cimma wadannan hadafofi na gama-gari da yake karkashin burin cimma samar da wannan jama’a tun daga rawa muhimmiya da wannan jama’a zata taka da wannan koyi kyakkywa zata bayar cikin jama’ar musulmi, kamar yadda zamu nuna nan gaba.

Ta haka ne ambaton samuwar koyi kyakkywa ya zo tare da wadannan siffofi gefe-da-gefe daura-da-daura, siffofi ne da ba makawa Shi’a su siffantu da su, kai an gwama wannan siffa da sashen wasu hadisai da abin da suke siffanta kawukansu da shi na daga siffa ta abin koyi.

A hadisin Umar Dan Yahaya ya ce: “Na ji Abu Abdullah yana cewa: “Mafi cancantar mutane da tsantseni su ne alayen Muhammad (A.S) da shi’arsu domin jama’a su yi koyi da suâ€‌[36].

Hadisi ya riga ya gabata daga Zaid Asshihaf wanda ya zo da shi daga imam Sadik: “Hakika mutum yan akasancewa daga kabila daga shi’ar Ali (A.S) sai ya zama adonta, ya fi su rikon amana, ya fi su bayar da hakkokin mutane, ya fi su gaskiya a magana, kuma wasiyyoyinsu da ajiye-ajiyensu gareshi ake bayarwa, jama’a tana tambaya game da shi sai a ce: Babu kamar wane! Hakika shi ya fi kowa rikon amana da gaskiyar zanceâ€‌[37].

Daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: “Hakika sahabban Ali (A.S) sun kasance ana kallonsu acikin kabilu, sun kasance ma’abota ajiye-ajiye, yardaddu gun mutaneâ€‌[38].

A wata ruwaya daga Sulaiman Dan Mihran ya ce: “Na shiga wajan Sadik Ja’afar dan Muhammad (A.S) a gunsa akwai wasu jam’a daga Shi’a sai ya ce: Ya ku jama’ar Shi’a, ku zama ado garemu, kada ku zama aibi akanmu, ku gaya wa mutane kyakkyawa ku kiyaye harsunanku, ku kame gabarin zancen banza da mummunan magana[39]â€‌.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next