Halayen Zamantakewa (A.S)



Na biyu: Amfani da hankali da yake shiryarwa zuwa ga gaskiya da binta, daga ciki akwai ilimi da sani, a daya bangren kuma akwai jahilci da son rai, da fadawa karkashin tasirinsu. Saboda haka ne azaba da lada suka zama daidai gwargwadon hankali, da kwadaitarwa a kan shawara da hankali da rinjayar da bangaren hankali a kan janibin sha’awa a al’amuran da mutum yake fuskanta a rayuwarsa.

Na uku: Tsoron Allah da kamewa da gyara kai yayin karkata zuwa ga sharri da sha’awa, da nisantar sabo da kuskure da zunubi, sannan da iyakance matsayin mutum da motsinsa wajan tarbiyyar rai, da kuma kiyaye karkatarta da kuma aiwatar da karfinsa a cikin iyakokin shari’a. Kuma samuwar alamomin cigaba ko tawaya na zatin mutum a rayuwarsa yana da alaka da wannan lizimtuwa ne.

Na hudu: Hakuri wajan biyayya da lizimtuwa da wajibai, da hakuri kan barin sabo da nisantar haram, da kuma dauke nauyin takurar rai ta waje, da kuma rashin yi mata saranda, da rashin karbar don abin da take so –rashin ba ta dama-, da kuma cigaba a tafarkin biyayya da nisantar sabo da karfafa abin da zai kawo hakuri, da kuma karfafa nufi da iko a kan juriya da kuma fin karfin rai, da tasirantuwa ta hanyar karfin nufi.

Na biyar: Yi wa rai hisabi da kuma lura da ayyukanta da take yi, da kuma kula da halaye, da ji a zuci, da sanin iyakacin yadda ya kai na dabbakuwa tsakanin aikinsa da abin da ya kudure na zuciyarsa, da shu’urinsa tare da huknce –hukncen shari’a da na kyawawan dabi’u din musulunci da siffofin kamala da kuma hadafi madaukaki da Allah madaukaki ya sanya ga mutum a tafiyarsa da motsinsa zuwa ga kamala.

Na shida: Tuba da koma wa zuwa ga Allah yayin fita daga tafarki madaidaici da tafarkin daidaito da alaci da fadawa zunubi da sabo ko aikata zunubai, da kuma gaggauta komawa zuwa ga Allah ta hanyar jin nadama, da furuci da laifinsa da niyyar lizimtar ayyukan shari’a, da kuma mayar da abin da ya zalunci mutane na dukiya da na abin da ya tauye musu na daga cin hakkinsu.

Na bakwai: Gano inda ake samun takurawar nan ta son rai, kamar son juciya da sha’awar mata, da tara â€کya’ya da dukiya na daga zinare da azurfa, da kuma dabi’u na rai na dan Adam kamar fushi da hassada da son shugabanci da girman kai da zato da kwadayi da kasala da kabilanci da nuna wariyar launin fata da â€کyan garanci da hamiyyar (ki ko so da aikin) jahiliyya, ko zalunci da ketare iyaka da cin hakkin wasu da sauransu, sannan kuma kokarin maganin wannan bayan an gano shi da fadakarwa a kan hakan.

Na takwas: Samar da wani makari da kuma dauki-ba-dadi da zuciyarsa da kame kai, da kula da kowane mataki daga matakai da zai iya takawa domin kamalar dan Adam a tarbiyyar ransa, wannan kuma yana iya samuwa ta hanyar lizimtuwa da wajibai da ladubba da mustahabbai da makruhai, ta yadda zai iya saka wata katanga da kariya da zasu hana ransa fadawa tasirin son rai, ya kuma samar da karin kamala na dan Adam.

Ana iya la’akari da cewa bayan wadannan tsarurrukan musulunci na gaba daya, a kwai tsarin yin addu’a da ambaton Allah da imamai (A.S) suka sanya, wanda ya hada da na rana da na dare, hade da himmantuwa da raya dare musamman darare na musamman kamar daren lailatul kadari, da na jumma’a, da idoji, da bukukuwan msuslucni (mauludin Annabi, da ranar aike, da idin gadir, da rabin watan sha’aban…dss), ko raya wasu ranaku na musmman kamar ranakun tara na farkon zulhajji, da ranakun tashrik, da idi biyu, da ranar gadir, da ranar mauludi, da ranar aike, da ranar ashura, da sauransu.

Haka nan tsarin salloli mustahabbai na musamman da ake danganta su zuwa ga ma’asumai sha hudu daya bayan daya, da sallar Ja’afar, da makamantansu, ko salloli na gaba daya na raya darare, da dararen Ramadan, da kuma bukukuwan musulunci.

Da tsarin wasu ibadoji kamar mustahabbai da ittikafi da hajjin mustahabbi, da umra, da ziyarar Annabi (S.A.W) da imamai (A.S) da salihai daga bayin Allah, da zikirori, da kuma ciyarwa a tafarkin Allah, da sadar da zumuncin makwabta da muminai, har ma da sadar da zumuncin dukkan musulmi.

Dukkan wannan akwai bayaninsa dalla-dalla da za a iya gani a littattafan hadisai, kamar babin tarbiyyar rai da zamantakewa, da â€کyan’uwantaka, da kuma aiki kyakkyawa, ta yadda sakamakon zai zama shi ne samun daukaka zuwa ga kyawawan dabi’u da lizimta da kuma da karfi da dagewa a matsayin dan Adam na daidaiku da zamantakewar al’umma na gaba daya, Wadanda da sannu zamu yi bayaninsu in Allah ya so a bahasin tsarin alamomi da ibadoji.


[1]- Wasa’ilus Shi’a 8: 399, b: 1 daga babobin zamantakewa, h5.
[2]- Karin bayani zai zo a babi na bakwai.
[3]- Zamu zo da Karin bayani a bahasin siyasa.
[4]- Zamu yi bayanin wannan a bahasin tsarin tsaron kasa.
[5]- Surar Nisa’i: 160. Akwai bayani dalla-dalla game da haka a babin hujja na wannan littafi.
[6]- Akwai wasu jama’a daga mabiya Ahlul Baiti (A.S) da aka san su da akhbariyyun da suke da ra’ayin cewa wasu littattafan sahihai ne gaba dayansu, sai dai a yanzu babu masu wannan ra’ayi.
[7]- Surar Anbiya: 105. 
[8]- Surar Nur: 55.
[9]- Dukkan al’umma tana da tunanin sauraron jiran imam mahadi (A.S) sai dai karfafa hakan a aikace ya kebanta da mabiya Ahlul Baiti (A.S).
[10]- Zamu yi magana game da akidar imam mahadi a babin sakafa, da kuma a babi na biyar a bayanin muhimmiyar gudmmuwar imamai daya bayan daya.
[11]- Alkafi 2:213, h2.
[12]- Alkisas: 56, Yunus:99, Alkafi: 2:213, h4.
[13]- Zamu yi Karin bayani a babin tsaro, kuma mun yi bayaninsa a babin hujja.
[14]- Alkafi 2: 18-19, da Wasa’ilus Shi’a 1:7, h2.
[15]- Amalis Saduk: 416, h548. da kuma Bihar 68: 9, h4.
[16]- Almu’ujamul Kabir 3:66, h2681, Tabarani, da Sawa’ikul muhrika: 228-229.
[17]- Mabiya Ahlul baiti (A.S) suna karbar hadisai daga wadanda ba mabiyansu ba idan sun rawaito daga dayan ma’asumai (A.S) matukar sun kasance masu wannan ruwayar amintattu ne.
[18]- wannan mas’ala duk da ta kasance an yi sabani a cikinta sai dai mafi yawa sun tafi a kan abin da muka ambata.
[19]- Sawa’ikul muhrika: 341, babin wasiyyar annabi da su, da Kanzul ummal 1:185-189.
a href="#_ftnref20" name="_ftn20">[20]- A’arafi: 96.
[21]- Uyunu akhbarir Rida 1: 261, h21.
[22]- Alkhisal 2, h4.
[23] - Al’irshad: 114, da Amali na Tusi: 216, h377.
[24] - Sifatus Shi’a: 118, h63.
[25] -Kanzul fawa’id 1: 87-88, da Bihar 68: 191, h47.
[26] -Kanzul fawa’id 1:88-92, Bihar 68: 192-196, h48.
[27] - Nahajul Balaga, Assalih, huduba: 193.
[28] - Assaffi: 2-3.
[29] - Gaiba Annu’umani: 113, b5, h7.
[30] - Tafsirin Imam Hasan Askari: 330.
[31] - Ikhtiyaru ma’arifatir rijal: 525, da Bihar 68: 166, h17.
[32] - Wasa’ilus Shi’a 11: 431, h1.
[33] - Masadarin da ya gabata , h3.
[34] - Masadarin da ya gabata: 435, h16, da Almahasin 1: 409, h930.
[35] - Masadarin da ya gabata: 435, h17. da Almahasin 1:409, h931.
[36] - Bisharatul Mustapha: 17.
[37] - Wasa’ilus Shi’a 8: 399.
[38] - Almishkat: 63.
[39] - Al’amali Tusi: 440, h987.
[40] - Kurbul Isnad: 78, H253. Da Bihar 68:149 B19, Sifatus Shi’a, H1.
[41] - Alkafi 2:637 h2, da kuma bihar 78:266, babin wa’azi na gaskiya, h178.
[42] - Almishkat: 62, h3.
[43] - kafi 2:236, h24.
[44] - wasa’ilus Shi’a 18: 12, h12.
[45] - wasa’ilus Shi’a 8: 542, b 122, h5.
[46] - A Duba Tattaunawa A Bihar J10 Da Littattafai Kamar Ihtijaj, Da Usulul Kafi Kitabul Imani Wal Kufr Da Kuma Ihtijaj Na Tabrasi, Kafa Hujjar Fadima (A.S) A kan Musulmi: 102. Da Kuma Kafa Hujjar Imam Ali (A.S) A kan Mutane A Game Da Yakin Basara: 169-170
[47] - alkafi 2: 24, h2.
[48] - wasa’ilus Shi’a 11: 446, h6.
[49] - kafi 1: 222, h2.
[50] - Masadarin da ya gabata: h3.
[51] - Masadarin da ya gabata: 225, h4.
[52] - kafi 1: 268, h9.
[53] - kanzul ummal 1: 185-189
[54] - komawa tafsirai, da kuma littafinmu muhadarat fi ulumul kur’ani.
[55] - kafi 1: 69, h3. da mahasin 1: 347, h127 da bihar 2: 242, h37.
[56] - mahasin 1: 347, h128 da bihar 2: 242, h38.
[57] - surar nahal: 75.
[58] - surar zumur: 39.
[59] - surar fusilat: 41.
[60] - Surar hujurati: 14-15.
[61] - Kafi 2: 26-27, h5.
[62] - kafi 2: 38, h6.
[63] - kafi 2: 38, h7.
[64] - kafi 2: 42, h1.
[65] - kafi 2: 45, h3.
[66] - surar ahzab: 21.
[67] - Surar Mumtahannati: 4.
[68] - Surar Mumtahannati: 6.
[69] - Surar Al’an’am: 89-90.
[70] - Surar Zuhurufi: 22.
[71] - Surar Ahzab: 67.
[72] - Surar Wasa’ilus Shi’a: 8: 513, h1.
[73] - Wasa’ilus Shi’a: 8:412, h4.
[74] - Alkhisal 1: 21, h62, da kuma bihar 71: 178, h25.
[75] - Daraja ce madaukakiya ta tsayuwa a kan tafarki madaidaici, ko kuma mallakar rai da zata iya hana mutum fadawa cikin haramun ko barin wajibi, ko kuma take sanya shi zuwa ga tuba daga abkawa cikin zunubi.
[76] - Mun yi bayanin wannan bahasi a tafsirin surar juma’ati kuma zamu yi Karin bayani a bahasin tsarin zamantakewar al’umma, da kuma tsarin ibadoji da alamomi.
[77] - Mun yi bincike a wannan maudu’i dalla-dalla a bayaninmu na Ramadan shekarar 1413 – 1414, ana kuma iya samu a babin tsarkake ruhi, da horo da kyakkyawa, da hani ga barin mummuna, da sauransu.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26