Halayen Zamantakewa (A.S)



Idan abin da na gaya maka ya Ahnaf ya tsere maka, to za a bar ka cikin kadarkon narkakkiyar darma na wuta, kuma wallahi za a yi dawafi da kai tsakaninta da tsakanin tafasasshen ruwa mai kuna, da sannu za a shayar da kai kunkunan a cikin mafi zogin nunar zafinsa, da yawa a wannan rana akwai tsatso da ake sawa takunkumi a baki da kuma fuska da za a kona, da kuma wanda ake lalata kamarsa a shafeta da kamar hancin giwa, ga nau’in sarkar wuta ta cinye tafinsa, kuma rataya da sakandami sun lauye wuyansa,, da ka gani ya Ahnaf ya yin da suke gangarowa daga kwararonta, suna hawa duwatsunta, an sanya musu kayan narkakkiyar darma, an hada su tare fajiranta da shaidanunta, idan suka nemi taimako da mafi muni sai a riko da azabar kuna da kunamunta da macizanta zasu kawo musu hari, da ka ga mai kira yana kira yana cewa:

Ya ku â€کyan aljanna da ni’imarta! ya ku ma’abota ado da kayan kawa! ku dawwama ba bu mutuwa. Yayin nan kaunarsu zata yanke, a kulle kofofin, dalili zai yanke, da yawa a wannan ranan zaka ga tsoho yana kira wayyo furfurata! (Wayyo tsufana na banza!) saurayi yana ihu wayyo samartakata ta banza! Da yawa daga mace tana ihun wayyo abin kunyana! An keta sitirarsu da mutuncinsu, da yawa a wannan rana wanda aka dulmuyar da shi tsaka-tsakin cikin hawa-hawa na wuta abin tsarewa, ya kaiconka da dulmuya da ta sanya maka tufafinka bayan tufafin katani, da ruwa mai sanyi a kan katangu, da kuma cin kala-kala na abinci, launi bayan launi na tufafi da ba zai bar maka wani gashi ba mai ni’ima da ka kasance ka ci shi sai ya mayar maka da shi fari, ko kuma wani ido da ka kasance kana gani zuwa ga wani masoyi da shi sai ya fasa shi, wannan shi ne abin da Allah ya tanadar wa mujrimai wancan kuma shi ne abin da Allah ya tanadarwa masu tsoron Allahâ€‌[24].

Haka nan wasu mahangai da Karaji ya rawaito a littafinsa “Alkanzâ€‌[25] a ruwayar Nauf albakali[26] daga Ali (A.S) a hadisinsa tare da wata jama’a daga sahabbansa daga cikinsu akawai Hammam dan Ubbada da Khusaim wacce Sharif Radi ya ambaci wani bangare nata a Nahajul Balaga[27].

Imani Da Wilaya Da Aiki

Dabbakuwa tsakanin da’awar shi’anci da wilaya ga Ahlul Baiti (A.S) da kuma bi a aikce garesu da kuma koyi da su duk wannan asasi yana daga mafi girman asasai da musulunci ya zo da su: “Ya ku wadanda ku ka yi imani domin me kuke fadar abin da ba kwa aiktawa. Laifi ya girmama a wajan Allah ku fadi abin da ba kwa aikatawa[28]â€‌. Kuma Ahlil Baiti (A.S) sun karfafa hakan yayin da suka damfara imani da aiki suna masu bayanin cewa cikar imani ba ya yiwuwa sai da aiki kamar yadda zamu nuna hakan a bincike masu zuwa.

Hakika ya zo daga Sadik (A.S) ce ya ce: “Ya kamata ga wanda ya ke da’awar wannan al’amari a boye ya zo da hujja a bayyane. Sai na ce: Menene hujja da zai zo da ita a bayyane? Sai ya ce: Ya halatta halal din Allah ya kuma haramta haram din Allah, ya kuma zama yana da zahiri da yake gaskata badininsa[29]â€‌.

Daga gareshi (A.S) kuma ya ce: “ba ya daga shi’armu wanda ya fada da harshensa yakuma saba mana a ayyukanmu da zantukanmu, sai dai shi’armu wanda ya yi daidai da mu da harshensa da zuciyarsa, ya bi zantuttukanmu ya yi aiki da ayyukanmu wadannan su ne shi’armu[30]â€‌.

Alkasshi ya rawaito da sanadi ingantacce daga Dawud dan Farkad ya ce: Na ji Abu Abdillahi (A.S) yana cewa: “Hakika sahabbaina su ne ma’abota hankali da takawa, wanda bai kasance daga ma’abaota hankali da takawa ba ba ya daga sahabbainaâ€‌[31].

Ikhlasi Ga Allah A Zuciya Da Aiki

Ihlasi ga Allah madaukaki a aiki da kuma a dabi’ar halitta da ji a zuci, haka nan -a motsi na daidaiku da kuma a alakar zamantakewa- da lizimtar asasin so don Allah da ki don Allah, yana mai nisanta daga tasirin duniya da kuma son rai.

Hakika imamai (A.S) sun karfafa wannan janibi da ake ce masa da riko da addini da imani na hakika da lizimtar akida na mutum musulmi, suka sanya wannan sifa ga shi’arsu a matsayin hadafi da ba makawa da kokari zuwa gare shi, ta hanyar dayawa daga hadisansu da suka yi bayani game da haka ko suka yi nuni da lizimtar hakan a aikace.

Kulaini ya rawaito da sanadi sahihi daga Abu Ubaida Alhazza, daga Abu Abdillahi Assddik (A.S) ya ce: “Wanda ya so don Allah ya ki don Allah ya bayar don Allah shi wannan yana dga wadanda imaninsa ya cikaâ€‌[32].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next