Halayen Zamantakewa (A.S)



Kuma daga imam Rida (A.S) ya ce: “Wanda ya so mai sabo shi ma mai sabo ne, wanda ya so mai biyayya shi ma mai biyayya ne, wanda ya taimaki azzalumi shi ma azzalumi ne, wanda ya ki taimakawa azzalumi shi adili ne. Ku sani babi wani kusanci na jini tsakanin Allah da wani, kuma ba a samun soyayyar Allah sai da biyayyaâ€‌.

Daga littafin Uyunu Akhbarir Rida daga Ibrahim dan Muhammad Alhamdani: “Wanda ya tabar da adili shi azzalumi neâ€‌ a cikinsa akwai cewa: “Ba wanda zai samu soyayyar Allahâ€‌ karshensa yana cewa: “hakika manzo (S.A.W) ya gaya wa bani Abdul Mudallib: Ku zo mini da ayyukanku ba da nasabarku ba. Ubanguiji yana cewa: “Idan aka yi busar kaho babu wani nasaba tsakaninsu ba a kuma tambayar su. Amma wanda ma’auninsa ya yi nauyi wadannan su ne masu rabauta. Amma wanda ma’aninsa ya yi sako-sako to wandannan su ne masu hasarar kawukansu suna masu dawwama a jahannamaâ€‌[48].

Haka nan rikon imaman Ahlul Baiti (A.S) ga usul ne ko a furu’a ba komai ne ba sai riko da mutum da yake siffantuwa da ilimi cikakke, da isa matukar mutumtakar dan Adam, da kuma isma daga sabo da isma daga kuskure a bayani, da kuma cancantar biyayya, da umarni da horo a aikace dalla-dalla.

Daga Abu Ja’afar (A.S) ya ce: “Ilimi da Allah ya saukar tare da Adam (A.S) ba a daukake shi ba, Ali ya kasance malamin wannan al’umma, kuma babi wani malami daga cikinmu da zai rasu sai wani malami ya maye gurbinsa daga zuriyarsa wanda ya san kwatankwacin abin da ya sani, ko abin da Allah ya soâ€‌[49].

Daga gareshi (A.S): “Hakika ilimi ana gadonsa, imami ba ya mutuwa sai ya bar wanda ya san kwatankwacin iliminsa ko abin da Allah ya soâ€‌[50].

Daga Darisul Kannasi ya ce: “Na kasance gun Abu Abdullah (A.S) a wajansa akwai Abu basir sai ya ce: “Hakika Dawud (A.S) ya gaji ilimin annabawa, Sulaiman ya gaji Dawuda, kuma Muhammad ya gaji Sulaiman, kuma mu mun gaji Muhammad (S.A.W), a wajanmu akwai suhufi Ibrahim (A.S) da allunan Musa (A.S), sai Abu Basir ya ce: Lallai wannan shi ne ilimi, sai Abu Muhammad ya ce: Wannan ba shi ne ilimi ba, kawai ilimi shi ne abin da yake faruwa da dare da rana, rana bayan rana, awa bayan awaâ€‌[51].

Riko da karbar hadisi daga garesu ba irin karba ne daga masu ruwaya ko mujtahidai ba wadanda suke da aikin cirato fatawa ko karbar ruwaya, kuma mutane suna komawa zuwa ga mujtahidan wajan sanin hukuncin shari’a ta hanyar cirato fatawa ba tare da ya zama suna da hakkin biyayya ta wilaya da shar’antawa ba a wannan fage, wannan ne abin da hadisan da suka nuna bayar da izini ga mujtahidai lokacin fakuwar imami (A.S) suke nuni zuwa gareshi, wadanda zamu yi nuni da wasusunsu nan gaba kadan, kamar yadda mujtahidai suke dogara a kan tunani suke iya samun kuskure ko mantuwa a fahimta ko kiyaye nasssi da fitar da hukunci daga gareshi, sabanin imamai (A.S) su kam suna da hakkin wilaya da iliminsu wanda yake na yakini yankakke.

Daga Muhammad dan Hasan Almaisami, daga Abu Abdillahi (A.S) ya ce: “Na ji shi yana cewa: Hakika Allah madaukaki ya tarbiyyatar da manzonsa har ya sanya shi a kan abin da ya ke so, sannan sai ya fawwala masa iko, madaukaki yana cewa: “Abin da manzo ya zo muku ku yi riko da shi abin da kuma ya hana ku ku hanu gabarinsaâ€‌. Kuma abin da Allah ya fawwala wa manzonsa (S.A.W) ya fawwala shi zuwa garemuâ€‌[52].

Saboda haka ne wannan jama’a ba ta bijiro wa batun rarrabewa da rinjayar wa ba game da umarnin da ya ke zuwa daga mahukumta da shugabannin al’umma na musulmi wacce malaman sunna suke ganainta a matsayin shari’a, domin saudayawa ta kan kasance daga tasirantuwa da son rai ne da dabi’ar halayen zuciya, ko kuma a yanayi na siyasa da ya kewaye su, shi ya sa wani lokaci sukan samu kansu a cikin kuskure wani lokaci, da kuma fatawar da mujtahidi yakan bayar dogaro da nassin kur’ani da kuma sunnar Annabi (S.A.W) ko komawa zuwa ga zato kamar ka’idar kiyasi da istihsani da masalihir mursala da makamantansu yayin da suke gajiya wa ga kaiwa zuwa ga nassin shari’a, ko su bayar da fatawarsu ta tunaninsu da zatonsu wani lokaci a maimakon nassi, kamar yadda ya zo a bahasin ijtihadi alhalin ga nassi, ta yadda suka zama suna hangensa ta mahangar istihsani ko masalihir mursala al’amuran da suke fahimta ta hanyar ganin yanayin tunani na zamantakewar al’umma. Saudayawa wadancan malamai suka fuskanci cutarwa da kamu ta bangaren shugabanni a wasu lokuta, al’marin da ya sanya sukan yi  magana mai karo da juna da kuma tanakudi, kamar yadda hakan ya faru ga Abu hanifa da ya shiga kurkuku da kuma kamu daga sarki Mansur saboda matsayinsa na siyasa a kan karfafa Yahaya dan Zaid, da kuma karfafa Muhammad da Ibrahim â€کya’yan Abdullahil mahad, haka nan Ahmad Dan Hambal saboda matsayinsa na al’amarin halittar kur’ani da kuma sabaninsa da Sarki Ma’amun a kan hakan.

Kamar yadda wannan jama’a ta gari ba ta rarrabe ba tsakanin malam kalam da na falsafar musulunci ma’abota nazari da kuma asasai na akida da suka yi sabani aciki sabani mai tsanani, da kuma fatawar da malamai suka bayar, saudayawa ba sa dora wa kansu damfaruwa da nazarin wannan ko na wancan.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next