Halayen Zamantakewa (A.S)



Sai ya ce: Ba ni labari game da imani, shin shi zance ne da aiki ko kuma zance ne ba aiki?.

Sai ya ce: Imani dukkansa aiki ne, zance sashen wannan aiki ne da wajabtawar Allah da ya bayyana a littafinsa, wanda haskensa bayyananne ne, hujjarsa tabbatacciya ce, littafi yana shaida wa da hakan yana kuma kira zuwa gareshi.

Sai na ce: Siffanta mini wannan har in fahimta?.

Sai ya ce: Imani haloli ne da darajoji da kuma hawa-hawa da matsayai, daga cikinsa akwai cikakke, da kuma tauyayye wanda tawayarsa take tukewa, da kuma mai daduwa da daduwarsa take rinjaye.

Sai na ce: Ashe imani yana cika yana daduwa yana kuma raguwa?.

Sai ya ce: Na’am.

Sai na ce: Yaya hakan yake?.

Sai ya ce: Hakika Allah madaukaki ya wajabta Imani a kan gabobin dan Adam ya kuma raba shi a gareta, ya kuma warwatsata a kansa, babi wata gaba sai ta kasance an wakilta mata imani da abin da ba a wakilta wa wata ba, daga cikinta akwai zuciyarsa da yake hankaltuwa da fahimta da ganewa da ita, wacce ita ce shugaba da gabobi ba sa aiki sai da ra’ayinta da umarninta, daga cikin akwai hannayensa da yake riko da su da kuma kafafunsa da yake tafiya da su, da kuma farjinsa da sha’awarsa take daga gareshi, da harshensa da littafi yake magana da shi, yake kuma shaida wa a kansa da shi, da kuma idanunsa da yake gani da su, da kuma kunnuwansa da yake ji da su.

Aka wajabta wa zuciya abin da ba a wajabta wa harshe ba, aka wajabta wa harshe abin da ba a wajabta wa idanu ba, aka wajabta wa idanu abin da ba a wajabta wa ji ba, aka wajabtawa ji abin da ba a wajabta wa hannaye ba, aka wajabata wa hannaye abin da ba a wajabta wa kafafu ba, aka wajbata wa kafafu abin da ba a wajabta wa farji ba, aka wajabta wa farji abin da ba a wajabta wa fuska ba.

Amma abin da aka wajabta wa zuciya na daga imani shi ne furuci da sani, da kuma gaskatawa da mika wuya, da kullawa, da yarda da cewa babi abin bautawa sai Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya gareshi, Samad (Tilo ne sidif) ne, bai riki abokiya ba ko da, kuma da shaidawa Muhammad (S.A.W) bawansa ne manzonsaâ€‌[63].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next