Halayen Zamantakewa (A.S)



Hakika Kulaini ya rawaito da sandinsa daga sabit dan sa’id ya ce: “Abu Abdillahi (A.S) ya ce da ni: ya Sabit, menene tsakaninku da mutane. Ku kame ga barin mutane, kada ku kira kowa zuwa al’amarinku, na rantse da Allah da mutanen sama da na kasa zasu hadu a kan su batar da bawa da Allah yake son shiryar da shi da ba zasu iya ba. Ku kame ga barin mutane kada dayanku ya ce da dan’uwansa da dan amminsa da makwabcinsa komai, hakika Allah idan yana son alhairi ga bawa sai ya tsarkake ruhinsa, ba ya jin komai na kyakkywa sai ya san shi, ko mummuna sai ya musa shi, sannan sai Allah ya jefa kalmar da al’amarinsa zai faru a cikin juciyarsa[11]â€‌.

Ba makawa cewa umarni da kamewa da hani gabarin kira ba komai ake nufi da shi ba sai saduwa da isuwa zuwa ga husuma da ba su a cikin wannan kira, kamar yadda ya zo a wani hadisin na Kulaini: “Kada ku yi husuma a addininku da mutane, domin husuma tana sanya ciwo a zuci, hakika Allah madaukaki ya ce da Annabinsa (S.A.W) “Kai ba ka iya shiryar da wanda kaso sai dai Allah shi ne yake shiryar da wanda ya soâ€‌. Ya kuma ce: “Shin kana tilasta mutane ne don har sai sun zama muminai[12]â€‌.

 Kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi na kawadaitarwa a kan kira yayin da sharuddan yin hakan suka cika da kuma dama da ba ta iya kaiwa ga husuma, domin kira zuwa ga gaskiya wajibi ne na shari’a[13].

Da wannan ne zai iya yiwuwa mu fahimci karfafawar Ahlul Baiti (A.S) kamar yadda ya zo a ruwayoyi a kan bayyana shika-shikan addini musamman ma nassi a kan wilaya, haka nan bambancewa tsakanin musulunci da Kafirci, da muslunci da imani, hakika dukkan wannan da makamantansa ya zo domin ya ikance alamomin akida sahihiya.

Shatin layin da yake bambance wa tsakanin akida ta gari gun jama’a saliha shi ne al’amarin son Ali da imamai (A.S) daga â€کya’yansa (A.S) da imani da wilayarsa, yayin da aka jingina akida ta gari da wannan wilaya a sashen ruwayoyi da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S)

Hakika ya zo a sanadi ingantacce daga Zurara daga Abu Ja’afar (A.S) ya ce: “An gina musulunci a kan abubuwa biyar: A kan salla, da zakka, da hajji, da azumi, da wilayaâ€‌.

Sai Zurara ya ce: Sai na ce: Wanne ne ya fi daga cikinsu? Sai ya ce: Wilaya ita tafi domin ita ce mabudinsu shugaba shi ne jagora akansu, sai na ce: Sannan wanne ne yake bin wannan a fifiku? Sai ya ce: Sallah, sai na ce: sannan wanne ne yake binta a fifiko? Ya ce: Zakka domin ita an gwama ta da ita, ya fara da salla Kafin ta, na ce: Wanne ne yake bin ta a fifiko? Ya ce: Hajji, na ce: Me yake bin sa? Ya ce: Azumi[14]â€‌.

A wata ruwaya da Saduk ya rawaito a littafinsa na Amali daga Abu Ja’afar Assumali daga Ali dan Husaini (A.S) ya ce: “Salman alfarisi (R.A) ya ce: na kasance ina zaune gun manzon Allah (S.A.W), sai Ali dan Abu Dalib (A.S) ya gabato, sai ya ce da shi: “Ya Ali ba na yi maka bishara ba?. Ya ce: Na’am ya manzon Allah, ya ce: Wannan masoyina Jibril ne yana ba ni labari daga Allah madaukaki cewa, ya ba wa masoyinka da shi’arka dabi’a bakwai: “Sauki gun mutuwa, da nutsuwa yayin dimuwa, da haske gun duhu, da aminci yayin tsoro, da adalci gun awon mizani, da wucewa kan siradi, da shiga aljanna Kafin sauran mutane da shekara tamanin[15]â€‌.

Ahlul Baiti (A.S) sun sanya alamomi masu yawa da isharori a kan wannan so da wilaya din, wanda daga cikn mafificiyarta kuma mafi girmanta su ne takawa, da ijtihadi, da hakuri a kan abubuwan ki, da sadaukarwa, wanda zayara imam Husaini (A.S) a karbala ta zo da bayani game da shi kamar yadda ruwayoyin suka zo da shi.

2- Komawa Zuwa Ga Ahlul Baiti (A.S) Don Sanin Addini

Hakika al’amarin lizimtuwa da isuwa zuwa ga hukuncin shari’a daga masdarinsa na asali ingantattu, haka nan samuwar matsayi na shari’a domin rarrabewa a cikin hukunci da husuma da kuma sababbin al’amura ta hanyar mutum na gari ko imami ma’asumi da malami adili, suna daga al’amura da wannan jama’a ta gari ta kebanta da shi. Domin duk da cewa musulmi gaba daya sun hadu a kan cewa kur’ani mai girma da sunnan Annabi su ne masdari na asasi na asali ga shari’ar musulunci, da mabiya Ahlil baiti (A.S) suka bambanta da shi a kan sauran musulmi a wannan fagage da zamu yi bayaninsu a cikin wadannan bayanai:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next