Halayen Zamantakewa (A.S)



HadinKanMusulmi

Rawar da shi’ar Ahlul Baiti (A.S) suka taka wajan kawo hadin kai tare da sauranr al’ummar musulmi da musulunci daga sauran mazhabobi, ta yadda ya kasance suna yin takiyya tare da sauran bangarori domin su saje, da kuma kafa ruhin dankon zumunci da rayuwa tare a tsakanin musulmi, da kuma karfafa dankon son juna tsakanin al’ummar musulmi.

Takiyya duk da ta kasance a daya bangarenta, ta tabbatarwa mabiya Ahlul Baiti (A.S) daya daga rukunonin kariya ga samuwarsu da kiyayesu daga ganin bayansu da makiyansu na daga sarakuna suke son su gani, sai dai takiyya ba a yi maganarta ba a koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ta wannan bangaren kawai, sai dai an yi maganarta ta wani bangaren, wanda shi ne tabbatar da hadinkai da sajewa da sauran al’ummar musulmi, shi ya sa sai ka same su suna kwadaitar da shi’arsu a kan samar da lamuni da daukar nauyi da cika alkawari da halartar jana’iza da masallaci da gaida maras lafiya tare da karfafa wa a kan rashin yiwuwar wadata daga barin mutane da bukatar su.

Hakika mabiya Ahlul Baiti (A.S) sun lizimci wannan wasiyyar, suka kuma yin amfani da ita a lokacin da suke da karfi kuma suka lizimce ta a lokacinda suke da rauni ko kuma lokacin da ake korarsu. Saboda haka ne ba a san wani abu game da Shi’a ba da suka yi na daga aikin kisa da kawarwa da batarwa kan sauran mazhabobi na musulunci, har a halayen da ya zama su ne suke rike da ragamar jagorancin al’amuran al’umma, sai dai sun kasance kodayaushe da’iman suna masu riko da tafarkin kariya ga ransu yayin da suke fuskantar gabar makiya a mafi munin lokuta, sukan kuma yi riko da hakuri da shiru da jurewa nau’o’in cutarwa da kuma danne hakkinsu na kashin kansu da tasirantuwa da wannan tafarki.

Kamar yadda ba su riki tafarkin tsanantawa da ta’addanci da hanyoyin kisa da kamawa da sacewa da garkuwa ko kashe wa da kishirwa da yunwa, amma su kam sun kasance karkashin dukkan wata mummunar hanya ta dabbanci da aka azabtar da su da ita, wacce take hadawa har da wadanda ba ruwansu daga cikinsu da raunanansu kamar mata da yara da tsofaffi.

Da sannu zamu zo da Karin bayani game da hanyar takiyya da tsarin kariya ga al’umma, sai dai ni zan duba nassi mai zuwa da imam Sadik yake iyakance daya daga cikin abubuwan da sakamakon takiyya yake haifarwa: Kulaini ya rawaito a cikin usul da sanadinsa daga Marazim daga Abu Abdillahi Asssadik ya ce: “Ina umartar ku da salla a masallaci da kyawon makwabtaka ga mutane da bayar da shaida da halartar jana’iza, ku sani ba makawa daga gareshi. Babi wani da yake bukatuwa ga barin mutane a rayuwarsa, kuma mutane ba makawa sashensu yana bukatar sashe[1]â€‌.

Asali Da Kuma Misali Mai Kyau

Al’amarin riko da asali da mutanen da suke misali na gari a cikin al’umma da kuma tsayawa a bangaren gaskiya da ka’idoji na asali na shari’a a tsakanin Shi’a mabiya Ahlul Baiti (A.S), ta yadda ya zama wani alami ne da suke siffantuwa da shi, kuma ya sanya su su rayu kodayaushe a bangaren asakala da hukuma, al’amarin da ya sanya su rasa da yawa daga dukiyar duniya da kuma zama karkashin zalunci, sai dan wannan al’amari da wannan tafarki, sun zama dalili muhimmi wajan kare al’umar musulmi da kimar ta da darajarta da koyinta na asali, ta hanyar motsar da mutum na gari wanda ya ke riko da gaskiya ya ke kuma tseratar da mutane duniya yake kuma kwadayin tabbatar da misali da hadafi mai girma.

Da yawa wani lokaci ya zama dama ta amu ga mabiya ahlul baiti (A.S) da su samu jituwa ta wani dan lokaci da tsari lalatacce domin su cimma wani hadafi na wani dan lokaci, kamar yadda ya faru a lokaccin abbasawa da suka kasance suna musharaka tare da su a wajan dauki-ba-dadi da umayyawa, kuma ya zama suna da alaka mai kyau da mabiya Ahlul Baiti (A.S), musamman cewa imamai (A.S) ba su dauki wani mataki na fada da hukumar abbasawa ba tun farko.

Haka nan sun samu damar hare-hare da suka sha tun farko a lokuta daban-daban, kamar a lokutan Magol da harin da makiya sukan kai wa kasashen musulmi kamar: Iraki da Labnon da sauran kasashen Khalij, da Yankin Indiyawa da Afganistan da sauransu. Balle kuma Iran yayin da aka samu damar taimakekeniya tare da sabon tunani na siyasa saboda mamayar nan ta wayewar yamma ga duniyar musulunci, wannan kuma domin samun kubuta daga zalunci da samun sabon matsayi na siyasa da na zamantakewa kamar yadda wasunsu suka yi.

Sai dai dayawa shi’ar ahlul baiti (A.S) sukan zAbu dauki-ba-dadi da lizimtar asasin addini, da juriyar haramta mu’amala da su da rashin kwanciyar hankali, tare da cewa sun zama su ne mafi yawa a wasu yankuna in an kwatanta da sauran jama’a ko kuma kai tsaye a su ne masu rinjaye a kashe-kashen wasu kasashen musulmi a wannan zamani.

Sai suka ki daukar wani mataki domin kansu suka lizimci wannan hanya da tafarki soboda wannan tarbiyya da suka samu ta riko da asalin da aka kafa addini a kansa, suka kuma siffantu da shi[2].



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next