JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Gadon baffanu a hannun dan diya.

 Abban ibn Abdilhamid  Lahiki ya ce:-

Ya’yan Abbas su ke da gado nai,

Baffa ga dan baffa ai hajibi ne.

  Mabiya Ahlulabaiti sai suka zabura saboda ji a jika cewa wannan furuci zalunci ne, suka yi raddi kan wadancan hujjoji da irin tunanin (mandiki) da aka yi amfani da shi a wani lokaci, a wani  zubin kuma su kan dauki wani mandikin dabam, daboda kafa hujja kan hakkin imaman Ahlulbaiti na imamanci. Daga wannan akwai kafa hujja da hadisin Gadir khummi kamar zancen Sayyid  Himyari, inda ya ce:-

  Wanda nake a gare shi shugaba,

Wannan tabbas a gare shi shugaba.

Amma sun ki yarda sun ki gamsuwa.

Muhammad ibn Yahya ibn Abi Murra Taglibi ya yi raddi kan hujjar mawakin

Abbasiyawa wanda  ya yi magana kan gadon baffanu, ya ce:-



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next