JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



 Safwul mali, zababbar dukiya, shi ne kayayyakin da suke da kima matuka daga cikin ganimar yaki. Da ba’a raba wa mayaka irin wadannan kayayyakin kamar yanda ake raba musu sauran dukiyar ganima saboda kada a fifita wani da  zababben abu, gudun kada wannan ya zamewa wani wata daraja ta karya. Maimakon haka ana barin irin wadannan kayayyaki ne a hannun shugaban musulunci ya yi amfani da su wajen abin da zai tabbabtar da maslahar musulmi gaba daya. Azzaluman mahukunta su kan dauki irin wannan dukiya su kebanta da ita ta hanyar kwace(gasabi). Imam yana fayyacewa kan cewa zababbar dukiya, wajibi ta zama tasu, haka nan ganima. Wannan yana nufin cewa Imam yana bayyana kansa a sarari a matsayin shugaban musulmi a ganin shari’a, wanda nauyin jujjuya wadannan dukiyoyi dai-dai da abin da yake ganin zai tabbatar da maslahar al’umma  a kansa yake.

A wani hadisin Imam Sadik (a.s) yana ambaton sunayen imamai magabatansa daya bayan daya, yana ba da shaidar imamancinsu da wajib cin biyayya gare su. Yayin da ya iso kan sunansa sai ya yi shiru, masu saurare kuma sun sani sarai cewa gadon ilmi da hikima bayan Imam Bakir (a.s) a wajen Imam Sadik (a.s) yake.  Kuma da wannan Imam (a.s) yake bayyan hakkinsa na jagorantar al’umma, yana bayyana  shi da wani salo mai danganta hakkin nasa da kakansa Ali ibn Abi Talib (a.s). Cikin wadansu babi-babi na littafin Alhujja cikin Alkafi da ma cikin juz’i na arba’in da bakwai na Biharul Anwar akwai irin wadannan hadisai da yawa, suna fayyacewa, wani zubin kuwa suna kinaya kan da’awar imamanci da kuma kira gare ta.

Domin tabbatar da wannan batu na tarihi, akwai hujjoji ko shaidu da suke tabbatar da samuwar wani tsararren shirin sadarwa da yake gudanar da kiran Imam (a.s) a ko ina cikin sassan duniyar musulunci. Mayawaitan hujjoji da ke akwai a kan wannan batu sun sa samuwar wannan shirin sadarwa wani al’amari ne yankakke ba wani shakka a kansa. Wadannan shaidun sun yi yawa da karfin da ana iya kafa hujja da su a kan wannan maudu’i namu, hujja tabbatatta, ko da ba’a sami sahihin  hadisi ko guda ba kan wannan batu.

Mu dubi  wadannan tabbatattun al’amuran tarihin:-

1.Akwai wata tsararrar alaka ta tunani da ta abin da ya shafi dukiya tsakanin imamai (a.s) da mabiyansu, kuma an kasance ana daukar dukiyoyi daga sassa dabam dabam na duniya ana kaiwa Madina kazalika da tambayoyin addini mayawaita.

2.Fadadar fagen da ke wilaya ga mutanen gidan Manzo (s.a.w.a) musamman a yankunan duniyar musulunci wadanda suke masu saurin daukar dumi.

3.Tattaruwar jama’a masana hadisi da maruwaita Kurasanawa da Sistanawa da Kufawa da Basarawa da Yamanawa da Misrawa gaban Imam (a.s).

Shin wannan al’amari wanda  sashensa yake munasaba da sajewa da sashe ya faru ne kwatsam ba tare da an shirya shi ba?

Wajibi ne mu yi kari da cewa wannan al’amari ya tabbata ne karkashin ikon siyasa wanda ya yi da gaske wajen watsi hatta da sunan Ali (a.s)  kai da ma zagin Ali a kan mimbarori da wanzar da nau’o’in dira da razanarwa kan mabiyansa. To a irin wannan halin, yaya aka iya samar da mabiya  mayawaita masu wilaya ga Ahlulbaiti  daga cikin talakawa suna taka dubban  milamilai saboda su kai kasar Hijaz da birnin Madina da zimmar daukar karatu gaban imaman Ahlulbaiti (a.s) da kuma koyon tunanin musulunci a kan rayuwar dai-daiku da ta jama’a da kuma tattaunawa da su kan batutuwa mayawaita da kuma mas’alolin tawaye wa yanayin barna da fasadi, ko kuma kamar yanda riwayoyi suke kiran al’amarin-mas’alolin ‘tsayawa’ da ‘ficewa’ daga da’a ga azzalumai )?!!

Idan da ace masu kiran Ahlulbaiti suna takaita bayanansu ne kan ilmin imamai (a.s) da zuhudunsu, to me ya sa tattaunawar wadannan mabiyan a kullum take kan batun tawaye ta hanyar daukar makami? Shin wannan baya nuni da samuwar  wani tsararren shirin sadarwa saboda kira zuwa imamancin  Ahlulbaiti (a.s) da cikakkiyar ma’anar imamanci, watau tsrin tunani da na siyasa?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next