JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



 

 

 

 

 

JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).

Imam Sadik (a.s) ya dauki nauyin ci gaba da wannan tafiya a cikin yanayi mai tsananin sarkakiya da wahala.

Bore ya kunno kai a ko ina a daular musulunci, hakimai sun shagaltu da tara kazamar dukiya alhali ga annoba da fari sun aukawa yanki mai yawa wanda ya hada da Kurasan da Irak. Masu mulki kuwa suna tursasawa da zalunci ba tare da rahama ba ko kankani, da haka suke jefa mutane cikin halin kaskanci da mika wuya. Kuma galibi hadarin masu shagaltuwa da ilmomin musulunci kamar fikihu da hadisi da tafsiri bai kasa na ‘yan siyasa da mahukunta ba. Alhali kuwa su ake tsammanin zamansu mafaka ga mutane. Yawa yawan wadannan malamai na kawata fatawowi saboda dadada wa sarki da hakimansa. Da yawa daga cikinsu suna shagaltar da kansu da ma mutane da mas’alolin da basu taka kara sun karya ba, suna ta da jayayyar da ba bakin komai take ba cikin mas’alolin ilmul kalam kuma babu abin da ya danganta ta da musulunci ko wahalhalun da al’umma ke ciki.

Nauyin da ya rataya a wuyan Imam Sadik (a.s) a wannan yanayi mai duhu shi ne abin da muka ambata kan sha’anin nauyin imamanci.A takaice shi ne bijiro da ingantaccen tunanin musulunci, watau bayyana musulunci kamar yanda ya zo cikin Alkur’ani dasunnarMa’aiki(s.a.w.a) gami da yaki da dukkanin baude-baude da gurbatarwar jahiliyya mai bin son rai. Haka nan kuma da shirya dabarun kafa tsarin adalcin musulunci da kuma kare wannan tsarin yayin kafa shi.Duk wannan nauye-nauye guda biyu watau nauyin wanzar da tsarin tunani da nauyin tsarin siyasa suna matsayin wani hadari mai girma ne ga tsarin da yake mulki. Ba nauyin siyasa kadai yake tunzura fushin sarauta ba, a’a shi ma nauyin tsarin tunani wanda yake jifa da baudaddun tunane-tunane da manufofin da sarki da  masu wa’azinsa ke gabatar wa al’umma da sunan addini, yana fusata ta. Wannan ya nuna cewa aikin kyautata tunani abin fifitawa ne domin yana kawar da karkatarwa da sunan addini wacce tsarin sarauta ke dogaro da ita wajen wanzarda zaluncin da yake yi wa jama’a. Ta wata fuska kuma yanayin da ake cikinsa a shirye yake ya saurari tunanin shi’a mai  neman sauyi, domin yaki da talauci da danniya sabubba ne masu habaka ruhin sauyi, ga kuma share fage da ayyukan Imam Bakir (a.s) suka yi a yankuna dabam-dabam. Dabarar cimma manufar Imamanci a game ita ce yunkurin sauyin tauhidi irin na Imam Ali. Bukatunta su ne:-Na farko: Samarda wata jama’a wacce za ta dauki tunanin imamanci, ta yanda zai saje da ita, sannan ta zama mai begen aiwatar da shi.

Na biyu: Samar da wata jama’a tsararriya mai jihadi da sadaukarwa. Shi kansa cimma wadannan bukatu yana bukatar yada kiran gaskiya a sassan duniya da shirya zukata domin karbar tunanin musulunci mai ra’ayin sauyi a dukkanin wurare. Har ila yau yana bukatar wani kiran daban wanda zai tanadi daidaiku masu sadaukarwa da fana’i, wadanda za su zama mambobin shirin tsare-tsaren kiran na sirri.Wannan shi ne sirrin wahalar kira bisa tafarkin imamancin gaskiya. Saboda kira mai dauke da sako, mai zimmar kawar da dagutu da fir’aunanci da jabberanci da dagawa da zalunci a cikin al’umma tare da cewa tana riko da ma’aunan musulunci wajen ayyukanta dole ne ta yi dogaro da zabin (irada) talakawa da karfinsu da imaninsu da nunarsu. Sabanin kiraye-kirayen da suke dauke da taken yaki da masu dagawa alhali su ma suna aikata irin ayyukan dagutai da azzalumai, basu lura da dokokin kyawawan dabi’u da na halin zaman jama’a. Irin wadannan kiraye-kiraye basu fuskantar wahalhalun da kira mai dauke da sako, mai manufa, take fuskanta. Wannan shine sirrin rashin tabbatar manufofin harakar Imamanci cikin gaggawa, shi ne kuma sirrin samun nasara nan take na harakokin da suka yi hannun riga da harakar imamanci, kamar ta Banu Abbas.

Yanayin da ake ciki da shirin da ayyukan imamin da ya gabata (Imam Bakir) bai shafi takwabi ba. A’a shi yana tsayawa ne ta hanyar suka mai tsanani, sawa’un da salon aikin gyaran tunani ko na tsare-tsare ko kuma ta wata fuskar dabam, da nufin kwankwasar azzalumai da yakar su. A nan Imam  Bakir (a.s) yana karfafawa kan ma’anar yukurin da Imam Sadik zai yi saboda aiwatar da babban nauyi wajen fuskantar mulki mai ci, kuma ba ya karfafawa kan sakamakon da ka iya biyowa baya. Kai a wata riwayar ma maganarsa kusan tana yanke kaunar samun nasarar harakar imamanci ne a cikin wannan yanayin siyasar da ake ciki.Daga cikin riwayoyin da a cikin su Imam Bakir (a.s) yake karfafawa kan rawar da Imam Sadik (a.s) zai taka akwai abin da Abu Sabah Alkinani ya ruwaito, ya ce: “Abu Ja’afar ya dubi dansa Abu Abdillah sai ya ce: ‘Kana ganin wannan?  Wannan yana cikin wadanda Allah Ta’ala ya ce (game da su :Kuma muna nufin Mu yi falala ga wadanda aka raunanar a cikin kasa kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magada.[1]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next