JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



A nan tambaya za ta zo kan cewa dalilin kawaicin tarihi dangane da samuwar irin wannan tsararren  shirin sadarwa a kiran Ahlulbaiti (a.s). Shin mene ne ya sa tarihi bai ambaci komai kan wannan batu a fayyace ba? Amsa ita ce abin nan da muka yi nuni da shi a baya. Ta yiwu  sahabban imamai sun lizimci ka’idar nan ta  hikima wajen haraka wanda aka sani da takiyya, wanda take ba ta  bada duk wani bare a tsarin imama damar kutsa kai. Haka kuma mai yiwuwa ne tarihi bai ce komai ba saboda rashin kaiwa harakar jihadi ta shi’a ga tabbatar da manufofinta da karbar ragamar mulki. Da a ce Banu Abbas  basu hau karagar mulki ba da kuwa, ba shakka duk bayanen aikace-aikacensu na sirri da muhimman batutuwan kiransu mai dadi da mara dadi da ya takaita ga zukatansu kadai, ba tare da wani ya san su ba kuma da tarihi bai rubuta komai a kansu ba.

Duk da haka riwayoyin da suke fayyacewa gwargwado kan samuwar mayalwacin kira zuwa ga imamancin Ahlulbaiti (a.s) ba kadan suke ba. Za mu hakura da guda daya mai cewa:-

Wani mutum daga mutanen Kufa ya zo Kurasan, sai ya kira mutane zuwa wilayar Jafar ibn Muhammad (a.s). Wata jama’a sai ta bi shi ta amsa kiransa. wata kuma ta musa masa ta yi inkari wata kuma ta dakata ta yi tsantseni. Sannan riyawar ta ce: Sai mutum daya daga kowace jama’a ya tafo wa Imam Abu Abdillahi (a.s). Mai magana daga cikinsu shi ne wannan da ya dakata ya yi tsantsenin. Sai ya ce : Allah ya kiyaye ka, wani mutum ya zo mana daga mutanen Kufa ya kira mutane zuwa biyayya da wilaya gare ka sai wasu mutane suka amsa masa, wasu suka yi inkari wasu kuma suka ya tsantseni suka dakata. Imam (a.s) ya ce:- “Daga cikin ukun wacce kake ciki? “Ya ce:- Daga jama’ar da ta yi tsantseni ta dakata. Ya ce: To ina tsantsenin ka yake daren kaza da kaza? (sai ya tunatar da shi kasawarsa a wani hali na sha’awa) sai mutumin ya yi shakka. [10]

Kamar yanda ka ji, mai kiran daga mutane Kufa yake, kiran nasa kuwa zuwa imamancin Ja’afar ibn Muhammad Al Sadik (a.s) da wilayarsa da kuma biyayya gare shi ne.

Akwai wadansu hujjoji daban masu bayyana abin da kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) da shi’arsu kan imamanci ya kunsa. Jayayya tsakaninsu da abokan hamayyarsu na siyasa (Umayyawa da Abbasiyawa) ta bijiro da shi. Wani lokaci ana wannan jayayya ne ta hanyar kafa hujja a fagen addini da ilmul kalam a wasu lokatan kuma tana daukar salon adabi mai zurfi ta hanyar wake. Duk jayayyar ana yin ta ne kan tabbatar da cancantar imamanci a siyasance da shugabanci ga imaman Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmaya  da masu kankamewa kan karagar hukumar musulmi bisa zalunci da kwace.  Saboda yin zamani daya da harakar Abbasiyawa da samun nasararta, lokacin Imam Sadik (a.s) ya kasance a cike yake da irin wannan jayayya da mujadala.

Mawakan Abbasiyawa suna kokarin tabbatar da cancantar shugabanci ga Abbasiyawa suna dogaro da hujjojinda, bisa al’ada, masu kwadayin mulki da kuma masu kankamo da karagar sarauta suke gabatarwa. Mawakan shi’a kuwa sukan  fuskance su suna gugar wadancan hujjojin suna masu kafa hujja kan fandarar da mulkin Abbasiyawa ya yi daga mandikin musulunci ( dalilan da ya dogara a kansu ) wanda yana kafe ne bisa yarfar da zalunci da aikata laifi da ha’intar hakkokin al’ummar musulunci.

  Mukabala ta hanyar wake tsakanin Abbasiyawa da Alawiyyawa  tana da muhimmanci a nan saboda irin muhimmiyar rawar da wake ke takawa a wancan lokacin wajen bayyana abin da rai ya kunsa da tunane-tunane saboda kuma irin tasirin da yake da shi kan mabiya cikin talakawa.  Ma’abocin littafin “Abbasiyawan Farko” yana ambatar rawar da adabi ya taka a karnin farko da na biyu. Ya ce:-

“Adabi ya kasance yana tasiri a zukata yana kokarin samun goyon bayan jama’a da karkatarsu ga wannan kungiya ko waccar, mawaka da masu jawabi matsayinsu irin wanda jaridu suke da shi a yau ne. Ko wannensu yana bayyana wani ra’ayin siyasa ne yana kuma kare wata kungiya ayyananna, yana bijiro da dalilin ingancikin kirar da yake yi daya bayan daya yana rushe ra’ayoyin abokan hamayya da magana mai tasiri da salo mai fasaha”[11]

Mawakan fadar Abbasiyawa sun kasance suna kokarin tabbatar da cancantar Abbasiyawa ga halifanci da hujjar alakarsu da Annabi ta hanyar ‘ya’yan baffa, sun kafa hujja kan hakan da cewa gado ba ya riskar ‘ya’yan diya tare da samuwar baffanu. Saboda haka halifanci a bayan Annabi hakkin Abbas, baffan Annabi ne, a bayansa kuma, na ‘ya’yansa ne, watau yayan Abbas. Marwan ibn Abi Hafsa ya ce:-

Kaka zai yiwu, ai bai yiwuwa,



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next