JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Bayan Imam Ali (a.s) ya karbi ragamar mulki shekara ta talatin da biyar bayan hijira mutane iri biyu suke tare da shi. Na farko sun san Imam da matsayinsa, sun fahimci ma’anar imamancin sun kuma gaskata shi. Wadannan su ne shi’arsa wadanda suka yi tarbiyya a gabansa ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar wadansu. Kashi na biyu ya kunshi jama’a baki daya wadanda suka rayu cikin yanayin tarbiyyar Imam da tafarkinsa amma basu da alaka ta tunani ko ta ruhi  da jama’ar da Imam ya yi wa tarbiyya ta musamman.

Saboda haka ne za ka sami mabiya Imam iri biyu ne na mutane, tsakaninsu da fifiko mai yawa. Kashi guda ya hada da Ammar da Malik Ashtar da Hujr ibn Adiy da Sahl ibn Hunaif da Kais ibn Sa’ad da tamkarsu. Daya kashin kuwa ya hada da Abu Musa AlAsh’ari da Ziyad ibn Abih da ire-irensu.

Bayan sulhin Imam Hassan (a.s) muhimmin matakin da Imam ya dauka shi ne yada tunanin mazhabin Ahlulbaiti da daidaita tsakanin masu wilaya da wannan tunanin, tun da an sami faragar motsawa mafi yalwa sabili da danniyar mulkin Umayyawa. Da’iman haka al’amarin yake, danniya tana kawo hadin kan wadanda ake dannewa ya sa su sajewa da kafuwa a maimakon watsewa da rarraba. Dabarun  Imam Hassan sun fuskanci tara karfi mai wilaya dan asali waje guda da kare shi daga rabkar tsarin Umayyawa, da kuma yada tunanin musulunci dan asali a tsakanin wata takaitacciyar kungiya, sai dai an zurfafa koyar da su wannan tunanin. Sauran ayyuka sun hada da neman masu  shigowa safun wilaya da dakon damar da ta dace da yin tawaye wa tsarin zalunci: da yin bindiga da ginshikansa da kuma aza hukuma Alawiyya a gubinsa. Wannan dabarar aiki ita ta bar Imam Hassan (a.s) da zabi daya kadai, wanda shi ne sulhu.

Wannan shi ya sa muke ganin wani gungun ‘yan shi’a karkashin jagorancin Musayyib ibn Najiyya da Sulaiman ibn Sard Alkhuza’i, ya tafo gurin Imam Hassan (a.s) a Madina bayan sulhu, yayin da ya dauki birnin ya zama cibiyar aikinsa na tunani da siyasa bayan dawowarsa daga Kufa. Wadannan mutane suna gabatarwa Imam da shawarar sabonta karfinsu da tsare-tsarensu na soji da mamayar Kufa da yin tafo-mu-gama da rundunar Sham. Imam ya yi kiran wadannan mutane biyu daga cikin gungun,  ya kebance da su, ya kuma tattauna da su kan abin da ba mu san me ya kunsa ba. Mutanen nan biyu sun fito a karshen wannan tattaunawa tare da cikakken gamsuwa da rashin alfanun daukar wannan mataki. Yayin da wadannan biyun suka koma ga wadanda suka zo tare da su sai suka fahimtar da su a takaice cewa an yi watsi da batun tawaye ta hanyar daukar makami, kuma dole  ne a koma Kufa domin a sake sabon aiki a can.[17]

Wannan muhimmin al’amari ya kunshi ma’anoni masu girma wadanda  suka sa sashen malaman tarihi na wannan zamani daukar wancan zama a matsayin tushen da aka kafa tsare-tsaren shi’a a kansa.

Hakikan al’amari shi ne idan dai matakin farko na tsare-tsaren shi’a an dauke shi ne a wancan zama tsakanin Imam Hassan (a.s) da mutane nan biyu wadanda suka tafi daga Irak to ai Imam Ali (a.s) ya yi wasici da irin wannan matakin a lokacin da ya yi wasici ga sahabbansa mukarrabai da cewa:-  “Idan kun rasa ni lallai za ku ga a bayana abubuwan da dayanku zai yi burin mutuwa saboda zalunci da gaba da son kai da rikon sakainar kashi da za’a yi  wa hakkin Allah da kuma tsoron abin da zai sami ransa. Idan haka ya faru :-

-Ku yi riko da igiyar Allah gaba dayanku, kuma kada ku rarraba…..

-Na hore ku da dauriya da kuma salla.

-Da kuma takiyya.

Kuma ku sani Allah Mai  girma da daukaka  yana kin bayinsa su zama masu fuska biyu. Kada ku gusa daga gaskiya da mutanenta domin duk wanda  ya musanya mu da wani ya halaka, kuma duniya ta kubuce masa, zai kuma fita daga cikin ta yana mai sabo)[18]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next