JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Kafin mu rufe wannan fasali ya dace mu yi nuni da wani salon kafa hujjan daban wanda kuwa shi ne salon wasika. Wadannan wasikun kafa hujja, a wani gefen, suna kunshe da bayanan manufofin kungiyoyi a sarari ba da wata rikitarwa ba. Ta wani gefen kuwa suna jan hankalin talakawa bayan yaduwar manufar bayanan. Kazalika ana samun tasiri mai karfi kan mataimaka da kuma abokan hamayya. Za mu ambaci wasikar da Muhammad ibn Abdillah ibn Hassan, Nafsi Zakiyya, ya aikewa Mansur sarkin Abbasiyawa. Wannan Ba’alawe mai neman juyi yana fayyacewa gaba gadi cewa yana fafutukar kwabe halifanci daga hannun abokin hamayyarsa domin ya kasanse a hannun ‘ya’yan Ali (a.s), ya ce:- “Lallai mahaifinmu Ali ya kasance shi ne wasiyyi kuma shi ne imami, to ta yaya kuka gaji shugabancinsa alhali ‘ya’yansa suna raye?”[12]

Ga alama Ba’alawen ya kawo wannan hujjan ne saboda raddi kan kafa hujja da Abbasiyawa suka yi kan gadar halifanci, domin banu Abbas  ba su mallaki wata hujja ba face wannan da’awar gadon. Nafsi zakkiya ya yi haka ne domin ya toshe musu duk wata kafa da irin nasu mandikin (salon hujja).

Ana iya lura a kalmominsa yanda yake karfafawa kan imammanci kana ya karfafa kan yanayin  kiran Gidan Ali wanda wannan mai neman juyin yake wakilta a wannan  jayayya.

2. Sharhi  kan hukunce-hukunce da tafsirin  Alkur’ani dai-dai da abin  da mazhabin  Ahlulbaiti (a.s) ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a).

  Wannan aikin shi ma ana iya ganinsa a rayuwar Imam Sadik (a.s) fiye da yanda ake iya ganin sa a rayuwar sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) abin da ma ya sanya ake kiran fikihun shi’a da sunan Fikhu Ja’fari kenan. Hatta masu rintsa ido kan ayyukan Imam Sadik na siyasa sun hadu kan cewa Imam ya  kasance yana gudanar da daya daga cikin mafi girman  makarantun fikihu a zamaninsa, idan ma ba mafi girmansu ba. Abin da bai gushe ba yana lullube ga barin idanun mafi yawan masu bincike kan rayuwar Imam shi ne ma’ana ta siyasa da ta gwagwarmaya wadanda irin wadannan ayyukan Imam suke dauke da shi. Wannan shi za mu kawo a yanzu.

Da farko ya zama wajibi mu ambata cewa mukamin halifanci a musulunci yana da wadansu sifofin da suke sanya shugaba ya banbanta da shugabanni a wadansu tsare-tsaren shugabanci na daban. Shi halifanci ba wai tsarin siyasa ne kadai ba a’a, shi tsari ne na siyasa da addini a gwame. Baiwa shugaban musulunci lakabin halifa yana karkafa wannan batu: shi halifan Manzon Allah (s.a.w.a) ne a duk wani aikin da Manzo yake aiwatarwa ga jama’a wa lau nauyin da ya shafi addini ne ko kuwa na jagorancin siyasa.

Shi halifa a musulunci yanan dauke da mas’u’liyyar siyasa da ta addini gaba daya. Wannan tabbataccen al’amari ya sa halifofin da suka zo bayan na farko, wadanda rabonsu a cikin ilmomi addini ya yi karanci ainun, ko kuwa basu da wani rabo sam, ya sanya su rufe wannan nakasu ta hanyar malaman addini  masu aikata musu abin da suke so. Sai suka baiwa fukaha’u da malaman tafsiri da na hadisi aiki a fada saboda tsarinsu na shugabanci ya tara sassan nan biyu: na addini da na siyasa.

Wata fa’idar samuwar masu wa’azin sarki a tsarin shugabanci, ita ce: azzalumin shugaba mai kama karya, a duk lokacin da ya so, yana iya canja wa hukunce-hukuncen addini fuska ko kuma ya musanya su dai-dai da bukatunsa. Wadancan ma’aikata, malaman fada, su suke aiwatar da wannan domin dadada wa masu azurta su. Suna yin haka ne karkashin rigar istinbadi da ijtihadi mai rudin jama’a.

Mawallafa da marubuta tarihi daga magabata sun ambato mana misalan da kare ba zai ci ba kan kirkirar hadisai da tafsiri da ra’ayi inda ake ganin hannun ikon siyasa a sarari. Za mu yi nuni da wani abu akai a nan gaba. Wannan al’amari wanda da farko(har zuwa karshen karnin farko bayan hijira) ya dauki salon kirkirar riwaya ko hadisi, sannu a hankali ya dauki matsayin fatawa. Daboda haka ne a karshen zamanin Banu Umayya da farkon na Banu Abbas muke ganin bayyanar fukaha’u masu yawa suna amfani da hanyoyin ka’idojin istinbadi masu rauni domin su kafa dokoki dai-dai da zabinsu wanda a kashin gaskiya zabin tsarin da yake shugabanci ne. A fagen tafsirin Alkur’an ma, kwatankwacin wannan aiki aka zartar. Tafsiri da ra’ayi, galibi, ya sa gaba wajen bayar da fahimce-fahimce wa musulunci, wadanda basu dogara da komai ba face zabin mai fassara da son ransa, wanda ba komai ba ne illa son ran tsarin da yake  shugabanci.

Wannan shi ne musabbabin rabuwar ilmomin musulunci: na fikihu da hadisi da tafsiri, tun zamunan na farko, zuwa ra’ayoyi biyu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next