JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Abin da littafin Jihadu Shi’a yake fadi gaskiya ne, inda ya yi taliki wa zancen Dabari da cewa:-

“Bayan kashe Imam Hussaini, jama’ar shi’a ta bayyana a matsayin wata jama’a  mai tsari, ra’ayoyin  addini da alakar siyasa suna dinke ta, tana gudanar da tararraki tana da shugabanni, kana tana da karfin soji. Jama’ar “Tawwabun” ita ce farkon mai bayyana dukkan wanna.

Bincike kan al’amuran  da suka auku a tarihi da ra’ayin marubuta tarihi kan wancan zamani, ga alama, yana nuna cewa shi’a suna daukar nauyin  jagoranci da shirye-shirye, sai dai farajiyar  fusata da sukar Banu Umayya ta fi  tsararriyar jama’ar shi’an nan fadi. Wannan farfajiyar tana haduwa da kowace  haraka mai rinin shi’a .

  Za mu gane cewa masu motsawa da hamayya kan Banu Umayya ko da sun yiamfani  da taken shi’a ba dai dai ne mu dauka cewa  dukkansu suna cikin adadin shi’a ba, watau adadin tsararren shirin nan na imaman Ahlulbaiti(a.s)  Bayan bayanin da ya gabata, ina son in yi ta’akidi kan  cewa  bayan shahadar  Imam Hussaini wadanda kadai ake kiransu shi’a su ne jama’ar nan da take da alaka mai karfi da imamin gaskiya, tamkar yanda lamarin yake a zamanin Amirul Muminina (a.s). Wannan jama’a ita ce bayan sulhun Imam Hassan (a.s) ta fuskanci kafa tsarin shi’a da umarnin Imam, kuma ita ce ta yi kokarin jawo mutane zuwa wannan tsarin da kuma kange mafiya yawa wadanda basu kai matuka a tunani ba kuma basu yi kwari a fagen aiki ba balle su kai matsayin shiga tsarin, wanda yake da zimmar samar da wata  babbar harakar shi’a.

Riwayar da muka kawo a farkon wannan bahasi wacce aka rawaito daga Imam Sadik (a.s) mai cewa adadin muminai bayan waki’ar Ashura bai wuce uku ko biyar ba, abin da take nufi shi ne ‘yan wannan kebantacciyar jama’a,watau mutanen nan da suke iya rawar gani, a matsayinsu na madugu mai wayewar kai  a kokarin kaiwa matuka cikin al’amarin juyin Alawiyyawa.

Sakamakon aikin da Imam Sajjad (a.s) ya yi a cikin sirri da tsanaki, turakun wannan ‘yar jama’a sun fadada kuma da wannan Imam Sadik (a.s) yake ishara a riwayar da muka ambata…… “sannan mutane suka risko su

  suka yawaita”. Za mu gani cewa zamanin Imam Sajjad da Imam Bakir da Imam Sadik ya ga motsawar wannan jama’a, wanda ta jefa tsoro da firgici  a zukatan azzaluman mahukunta, al’amarin da ya gamu da mai da martani mai tsanani.

A takaice, a karnin farko da na biyu bayan hijira da ma tsawon zamanin imamai (a.s) ba’a kiran wadanda suke kaunar Ahlubaiti da imani da hakkinsu da gaskiyar kiransu kadai ba tare da yin tarayya a tafiyar harakarsu ba da sunan shi’a. Su shi’a suna bambanta da saura ne ta hanyar wani tabbatanccen sharadi na tushe, wanda shi ne alaka da Imam wajen tunani da aiki da tarayya a aikin tunani da siyasa kai da ma ta fuskar aikin soji wanda yake jagoranta saboda  dawo da hakki ga mai shi da kafa tsarin Alawiyyawa na musulunci. Wannan alaka ita ake kira “wilaya” a kamus na shi’a.

Bisa hakika jama’ar shi’a  suna ne wanda ake baiwa ‘yan jam’iyyar imamanci, jama’iyyar da take motsawa karkashin jagorancin Imam (a.s) take kuma daukar boyewa da takiyya a matsayin mafaka, tamkar duk wata jam’iyya ko shiri mai rayuwar cikin tsoro da danniya.  Wannan shi ne takaitaccen  bayani kan dubi na hakika kan rayuwar Imamai (a.s) musamman  Imam Sadik (a.s) kuma kamar dai yanda muka ambata tun farko ba zai yiwu a sami hujjoji bayyanannu kan irin wannan al’amarin ba, tun da  ba za mu yi tsammanin za’a kafa wa wani gidan sirri alama mai cewa: “wannan gidan sirri ne” ba! Kazalika ba zai yiwu mu natsu da sakamakon (bincike) ba, ba  tare da samuwar wasu tabbatattun shaidun yanayi ba.

Saboda haka ya kamata mu bi biddigin wadannan shaidu da isharori.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next