JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Sai mai riwaya ya tambayi Imam ya ce:-  Shin makamin yana rabuwa da ilmi?

Imam ya ce:- A’a (watau jagorantar al’ummar musulmi wajibine ta zama a hannun wanda yake rike da makami da kuma ilmi gaba daya). Saboda haka Imam (a.s) yana ganin cewa ilmin addini da fahimtar Alkur’ani ingantacciyar fahimta daya daga sharudan imamanci ne. Ta wata fuska kuma ta hanyar aikinsa na ilmi da tara adadi mai yawa na masu kishirwa da begen  ilmomin addini a gangarsa, da koyar da addini yanda ya saba, cikakkiyar sabawa, da hanyar da aka saba wajen malamai da masana hadisi da masana tafsiri masu alaka da tsarin halifanci. Wannan yana tabbatarwa, a aikace, da cewa janibin addini sifa ce ta asali a makarantarsa, da kuma cewa rigar addinin da tsarin halifanci da malaman fada masu daka rawarsu ke da shi ta boge ce. Da wannan hanyar hari mai tsanani mara yankewa kuma cikin tsanaki Imam yake baiwa jihadinsa wata sabuwar kusurwa.

Kamar yanda muka ambata a baya, mahukuntan Abbasiyawa na farko wandanda suka sami shekaru da dama kafin su karbi mulki, sun kasance suna tare da jihadin Alawiyawa kuma mataimakansu suna da masaniya kan da yawa daga hanyoyi da sako-sako na kiran. Sun riski rawar da hari da fama da wannan aikin fikihu da hadisi da tafsiri ke takawa fiye da magabatansu, Umayyawa. Hala wannan dalilin shi ya sanya Mansur, saboda tinkarar Imam Sadik (a.s) ya hana shi zama a halakar koyarwa na wani lokaci da hana mutane zuwa gare shi. Har Mufaddal ibn Umar yana cewa:- “ Hakika Mansur ya daura aniyar kashe Abu Abdillah ba ma sau daya ba, ko yaushe ya aika a kira shi domin ya kashe shi, idan ya dube shi sai haibar Imam ta rufe shi kana ya bar shi, sai dai fa ya hana mutane zuwa gare shi, ya kuma hana shi zama saboda mutane, ya bincike shi bincike mai tsanani, har al’amarin ya kai ga cewa waninsu zai bukaci samun haske a wata mas’alar addini kan batun aure ko shika ko wani abin  daban, gashi basu da sanin ta, kuma  basu iya isa gare shi. Sai mutum ya kaurace wa iyalinsa.  Wannan abu ya kuntata wa shi’arsa ya kuma yi musu tsananin”[16]

3. Kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa.

Ya gabata cewa Imam Sadik (a.s) a karshen zamanin Umayyawa ya jagoranci wani shirin sadarwa da sanarwa mai fadi wanda kuma manufarsa ita ce kira zuwa imamanci irin na  Ali (a.s) da bayyana sha’anin  imamanci a kan sahihiyar ma’anarsa. Wannan shirin sadarwa ya yi yunkurin tabbatar da aikin yada ma’anonin imamanci. Wannan yunkuri  ya yi alfanu saboda irin tasirinsa a sassan duniyar musulunci masu nisa masamman a Irak da Kurasan.

A nan za mu yi ishara ga kadan daga  wannan al’amari. Sha’anin tsaren-tsaren sirri a rayuwar siyasa ta Imam Sadik (a.s) da sauran imamai yana daga cikin al’amura wadanda suka fi muhimmanci kuma suka fi tsanani ko hadari, a lokaci guda kuma shi ya fi komai zama dishi-dishi da rashin bayyana a rayuwarsu. Kamar yanda muka ambata ba zai yi yu mu sami bayanin wannan al’amari a fayyace ba tun da ba mu tsammanin Imam ko wani daga sahabbansa zai yi furuci da cewa akwai wadannan tsare-tsaren siyasa da tunani a fili.

Wannan abu ne wanda ba za a iya gano shi ba. Abin da hankali zai kama shi ne Imam ya tabbatar da rashin samuwar irin wannan tsari na sirri, tare da musantawa mai tsanani, haka nan ma sahabbansa, kuma sun dauka wannan wata tuhuma ce da mugun zato da tsarin hukuma zai nemi su ba da bayani kan ta. Wannan  ita ce sifar da aikin sirri ya kebanta da ita, kuma shi ma mai bincike yana da damar  rashin  gamsuwa da samuwar irin wanna tsarin  idan ba da dalili mai gamsarwa ba. Idan haka ne to  ya zama wajibi mu bincika da shaidu da abubuwan da suka auku wadanda ga alama ba bakin komai suke ba kuma basu daukar hankalin mai karatu mara lura, saboda mu yi binciken manuniyar da suke da ita a kan wannan batu. Da irin wannan bin diddigi a rayuwa imamai (a.s) cikin karni biyu da rabi, mai bincike zai iya natsuwa da samuwar irin wadannan tsare-tsare masu aiki karkashin jagorancin imamai (a.s).

Me ake nufi da tsari?  Ba fa tsari a nan yana nufin  wata jam’iyya tsararra bisa irin manufar da take da ita a yau ba. Ba kuma samuwar wasu dakaru tanadaddu masu jagorantar larduna, masu dangantaka tamkar tsarin dala ba. Babu wannan, kuma bai yiwuwa a same shi. Abin nufi da tsari shi ne samuwar wata jama’a ta bil Adama mai tarayya kan wata manufa, masu aikace-aikace daban-daban wadanda cimma waccan manufa shi suka sa gaba, masu alaka da matattara daya da zuciya mai bugawa guda daya da kwakwalwa mai tunani guda daya, sannan daidaikunta suna tarayya a alakar soyayya.

Wannan  jama’a, a zamanin Imam Ali (a.s) (watau cikin shekara ishirin da biyar tsakanin wafatin Manzon tsira da mubaya’ar Ali a matsayin halifa) ta kasance imani da hakkin Imam Ali na halifanci yana hada ta. Ta kan bayyana cika alkawarinta ga Imam ta hanyar tunani da ta siyasa, sai dai ita tana koyi da Imam Ali (a.s) kan rashin tada abin da zai girgiza jaririyar al’ummar musulunci. Haka kuma suna yunkurawa kan abin da a wadancan shekaru Imam Ali yake yunkuri saboda shi kamar nauye-nauyen sako da zimmar kare musulunci da yada shi da kokarin takaita baude-baude. Saboda wilayar ta wannan jama’a ta dauki sunan ‘Shi’ar Ali’.

Wadanda suka shahara daga cikinsu akwai Salman da Ammar da Abu Zarri da Ubayy ibn Ka’ab da Mikdad, da  Huzaifa da sauransu, daga manyan sahabbai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next