JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Tun lokacin da ya karbi nauyin shugabaci har zuwa wafatinsa, Imam ya dauki shekara talatin da uku yana jihadi maras yankewa. Cikin wadannan shekarun yanayi ya kasance yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana hawa da kuma sauka;wani zubi ya dace da maslahar mazhabin Ahlulbaiti, wani zubin kuwa yanayin ya juya akasin hakan. Wani lokaci halin yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana tsanani, har sahabban Imam su zaci cewa dukkan buri ya tarwatse. A duk wadannan halaye Imam Sadik(a.s) yana rike da ragamar jagoranci kyam tare da azama da jajircewa. Yana keta fagen nan mai rudani, mai tattare da tsammani da kuma yanke kauna, ba ya damuwa da komai sai tafiyar da ke

  gaba yana wanzar da kokari da karfin gwiwa da imani wa mabiyansa domin kaiwa ga tsira.

A nan ya zama wajibi mu yi nuni da wani al’amari mai ban takaici wanda dukkan masu bincike kan rayuwar Imam Sadik(a.s) suke fuskanta .

Wannan kuwa shi ne halin rashin tabbas wanda ya lullube shekarun farkon imamanci Sadik(a.s) wadanda suka yi muni daidai da karshen zamanin Banu Umayya. A lokacin rayuwa ba ta san natsuwa ba tana kuma cike da aukuwar manya-manyan al’amura,muna iya fahimtar alamunsu cikin daruruwan riwayoyi. Sai dai malaman tarihi da hadisi basu kawo mana labarin wannan lokacin a jere tare da sajewa da daganta wannan bayani da wancan ba. Saboda haka ya zama dole ga mai bincike ya yi dogaro da kuma lura da al’amura da suke baiyana cikin abinda yake karantawa (kara’in), ya lura da kungiyoyi da ra’ayoyi a game na wancan zamani sannan ya kwatanta ko wace riwaya da bayanan da ya riga ya sani domin ya ga abin fahimtar(mafhumi) abinda riwayar ta kunsa da rabe-raben ta.

La’alla daya daga dalilan wannan rikitarwa shi ne kasancewa harakar Imam da mabiyansa an yi ta cikin sirri, domin shiri na siri wanda ya kafu bisa ingantattun ginshikai dole ne bayanan da suka dangance shi su wanzu cikin sirri da boyewa, kuma wajibi ne kada wanda yake waje da wannan shiri ya tsinkaye su. Wadannan bayanai ba su watsuwa sai bayan tabbatar harakar da kuma nasararta. Saboda haka ne muke samun cikakkun bayanai dalla-dalla kan sadarwa ta sirri a harakar Abbasiyawa domin harakarsu ta yi nasara.  Babu shakka da an kaddara wa harakar Ahlulbaiti kaiwa ga nasara da karbar ragamar mulki da a yau mun riski sirrin tsare-tsarenta masu fadi.

  Akwai wani dalilin daban wanda zai iya janyo wannan rashin baiyana dangane da harakar Ahlulbaiti, cewa murubuta tarihi, bisa al’ada suna rubuta abin da yake dadada wa sarakuna ne. Domin haka muke ganin bayanai filla-filla kan rayuwar halifofi da wasanninsu da hirarrakinsu da wuraren holewarsu amma bamu ganin bayanan kirki kan masu neman juyi da wadanda aka zalunta da wadanda aka murkushe. Domin samun irin wadannan bayanan mai bin diddigi na bukatar dogon bincike da kirkado da tsananin biyawa. Amma rayuwar halifofi bayani ne tanadadde, tsuntsu daga sama gasashshe, yana kawo yardarsu da tarin kyaututtuka.

Marubuta tarihi masu rusnawa ga halifofin Abbasiyawa sun ci gaba da rubutu bisa wannan hanya na tsawon shekara dari biyar bayan rayuwar Imam Sadik (a.s). Saboda haka  ba za mu yi tsammanin samun wani abin kirki na bayanai kan rayuwar Imam Sadik (a.s) ba, da ma na ko wani imamin shi’a cikin wadannan littafai.

Hanyar kadai da za ta iya shiryar da mu kan layin da rayuwar Imam Sadik ta duka ita ce gano muhimman alamu na rayuwar Imam ta hanyar ka’idoji, a game, na salon tunanin Imam da dabi’unsa. Kana mu yi bincike kan abubuwan tarihi da suka danganci wannan rayuwa da hujjojin tarihi da suke warwatse da kuma irin wadancan abubuwa masu dangantaka da rayuwar Imam wadanda ba na tarihi ba har mu kai ga rarrabewar al’amarin filla-filla.

ALAMOMI A RAYUWAR IMAM SADIK (A.S).

Muhimman alamomi wadanda suke fitattu a rayuwar Imam Sadik (a.s)  idan muka lura da mahangar bahasinmu, suna iya tattaruwa cikin wadannan:-



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next