JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Kurayen Umayya su kira su azazzala,

Tuttudar kunci, da  masifu kansu ne.

Banu Abbasin dinu su barnata,

Ha’inci,  zalunci, halinsu ne.

Wai shi Rashidu saboda shiriya tasa

Mamun, Amin ka ga fa nasu ne.

Shiriya! Wanga bai tsare hakki ko daya.

Amincin su  zago ga Islama ne.

Ba abu ne mawuyaci ba ga mai bincike a kan farkon zamanin Abbasiyawa samun daruruwan misalai kan muhawarori da mukabalar siyasa wadanda suka kai yawan wake-waken da aka yi kan wannan batu. Mawakan shi’a da abokan hamayyarsu su kan kafa hujjoji ne kan kiran da kowannensu yake yi. Ba shi da muhimanci  mu san ingancin hujjojin da ake kafawa a wannan jayayya, abin da yake da muhimmanci shi ne mu gane ginshikin jayayyar da ake yi da kuma hakkin da sassan biyun ke da’awarsa. Akwai wani hakkin da ko wani sashe yake da’awa wannan kuwa shi ne gadar Manzon Allah (s.w.a) wajen mulki da jagorancin musulmi.

Jayayyar tsakanin sashen Alawiyawa da na Abbasiyawa ba kan gadar tadodi da dabi’u na gari da ma’nawiyya ko tsarin tunani irin na Annabi (s.a.w.a) ba ne. Ba wai ana sassabawa kan wane ne ya cancanci gadon wata tada ba ne, domin wadannan tadodi ba wani hakki ne da bangare biyun za su yi sa-in-sa a kai ba. Jayayyar dai a kan wani hakki ne  wanda sassan biyu suke da’awarsa. Kuma mun ji yanda mawaka a zamanin Imam Sadik (a.s) suke kare hakkin imami na jagorancin musulmar al’umman nan ma na mulkar jama’ar musulunci. Suna kuma kutsawa cikin yaki da wadanda basu da cancantar mulkar musulmi. Akwai shaidu masu yawa kan wannan batu a wake-waken karni na biyu bayan hijjira.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next