JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Ra’ayin na Biyu:- Ra’ayi dan asali amintacce wanda ba ya ganin akwai wata  maslaha mai daraja da daukaka da ta wuce bayyana ingantattun hukunce-hukuncen Ubangiji. Wannan ra’ayi ya kasance, ko an ki ko an so, yana cin karo da tsarin da yake shugabanci da kuma masu wa’azin fada, a duk wani taku da ya yi. Saboda haka tun farkon al’amari ya dauki mafuskanta irin ta talakawa tare da taka tsan- tsan  da kiyayewa.

Fahimtar wannan zai sa mu gane da kyau cewa sabawan Fikihun Ja’afar da fukaha’un sarauta a zamanin Imam Sadik ba wai sabawa ce ta tunani da akida kadai ba, a’a ta hada har da abin da ya kunsa na hari irin wanda abokin hamayya yake yi.

Mafi muhimmanci daga kusurwowin wannan abin da ya kunsa shi ne tabbatar da cewa tsarin da ke shugabanci fanko ne kawai wanda ya rasa dukkan ma’anonin addini, ga kuma gajiyawarsa  wajen gudanar da al’amuran tunani ga al’umma. Ko kuma mu ce rashin cancantarsa hawa mukamin “halifanci”. Wata kusurwa ita ce ayyana wuraren da aka baude cikin fikihun sarauta, wadannan baude-baude da aka gina kan tunanin “maslaha”  wajen bayanin hukunce-hukuncen fikihu da sassautarwar malaman fikihu ga tsarin da ke shugabanci. Imam Sadik (a.s), da ayyukansa na karantarwa da kuma sabar nauyin bayyana hukunce-hukuncen fikihu da ilmomin musulunci  da tafsirin Alkur’ani ta hanyar da ta saba da ta masu wa’azin fada, hakika, a aikace, ya dauki matsayin hamayya da tsarin da ke mulki. Da wannan aikin, Imam ya iya watsi da duk tsarin sarauta a addini da fikihu wanda wani bangare ne na hukumar halifofi, ya kuma tube wa tsarin da ke mulki duk wata rigar addini.

Ba mu da wani tabbataceen isnadi mai bayyana lurar tsarin Umayyawa da wannan janibin hamayya, wanda Imam Sadik (a.s) ya aiwatar a fagen ilmi da fikihu. Sai dai abin da aka fi tsammani shi ne tsarin Abbasiyawa mai mulki-----musamman lokacin Mansur wanda yake mai wayo ne da gogewa da fahimtar halayyar duniya, abubuwan da ya koya a lokacin dambarwar siyasa mai tsawo tsakaninsa da mulkin Umayyawa kafin shi kansa ya sami mulkin--wannan tsarin nasu yana riskar mas’alolin masu wuyar fahimta da ke tattare da ayyukan gidan Ali. Kuma tsarin Abbasiyawa  mai mulki yana fahimtar muhimmiyar rawar da wancan aikin ilmi zai iya takawa  ta bayan fage.

Barazana da kuntatawa da matsin lamba wadanda suke tattare da ayyukan Imam Sadik (a.s) na ilmantarwa wadanda kuma riwayoyi masu yawa na tarihi ke nakalto mana,  sakamakon wannan luran ne da kasancewar mas’alar mai hadari ce. Kazalika muhimmancin da Mansur ya bayar wajen tara mashahuran fukaha’u daga Hijaz da Irak a hedkwatarsa, kamar dai yanda nassoshin tarihi mayawaita suke nunawa, shi ma ya samo asali ne daga wancan lurar da ya yi.

A maganarsa da koyarwarsa ga sahabbansa da mukarrabansa, Imam (a.s) yana kafa hujja da “yanayin holoko da jahilci na halifofi” kan cewa a ra’ayin musulunci basu cancantar shugabanci. Ana iya ganin wannan sigar suka kan tsari mai mulki a sarari da fayyacewa  a darusansa na fikihu.

An ruwaito zancensa (a.s):- “Mu mutane ne wadanda Allah ya farlanta biyayya gare mu,  kuma kuna koyi da wanda ba’a yi wa mutane hanzari saboda jahilcinsa”[13]

Abin nufi shi ne mutane sun baude saboda jahilcin mahukuntansu da shugabanninsu, sun dauki wata hanya ba ta Allah ba. Wadannan ba abin yi wa hanzari ba ne wajen Allah domin biyayyarsu ga wadannan mahukunta aiki ne na baudiya saboda haka ba zai wanke abin da ke biyo bayansa na abkawa cikin baude-baude ba.[14]

A koyarwar imamai ( a.s) kafin imam Sadik da bayansa kuna ganin karfafawa kan wajibcin gwama  jagorancin siyasa da tunani da manufa (aidiyolojiyya). A wata riwaya daga Imam Ali ibn Musa Al Rida (a.s) daga kakansa Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce:  Makami a gare mu tamkar akwati ne ga Bani Isra’ila, duk inda akwati ya juya, sai mulki ya juya, (ka yi tunani da kyau kan ma’ana irin ta alama (ramzu) da ke cikin maganar) duk kuwa inda makami ya juya a cikinmu ilmi can zai juya. A wata riwayar kuma duk inda makami ya juya a cikinmu, to can al’amarin (hukuncin) yake. [15]

Sai mai riwaya ya tambayi Imam ya ce:-  Shin makamin yana rabuwa da ilmi?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next