JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



 La’alla wadannan fayyace-fayyacen Imam Bakir su ne suka yada tunanin yunkurin Imam Sadik (a.s) da halifancinsa a tsakanin ‘yan shi’a, ya kuma sanya sahabban Imam Bakir da Imam sadik(a.s) sauraron wata faraga daga lokaci zuwa lokaci. Akwai wata riwaya cikin Rijal na Shaikh Kashshi wacce a cikinta ana iya fahimtar wannan yanayi mai wanzuwa a tsakanin mabiya Ahlulbaiti a wancan lokacin. Ibn Miskan ya ruwaito daga Zurara cewa ya tambayi Abu Abdillah (a.s) batun wani mutum cikin abokanmu wanda yake buya saboda gudun tara. Ya ce: Allah ya kiyaye ka! Akwai wani mutum cikin abokanmu yana buya saboda gudun tara, idan wannan al’amari kusa yake zai hakura har ya fito tare da mai tsayawa, Idan kuma akwai jinkiri zai yi sulhu ( da mahukunta ) saboda gudun tara. Sai Abu Abdillah (a.s) ya  ce: Zai kasance. Sai Zurara ya ce : Zai kasance nan da shekara? Sai Abu Abdillah ya ce: Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara ya ce: Zai kasance nan da shekara biyu? Sai Abu abdillah ya ce: Zai kasance insha’allahu. Sai Zurara ya fita, sai ya kwallafa ransa kan cewa zai kasance nan da shekara biyu. Amma bai faru ba. Sai ya ce : Ban kasance ina ganin Jafar ba face ya fi haka sani.[2]

Kalamar ‘wannan al’amari’ a sanin mabiya Ahlulbaiti kinaya ce kan zamani mai zuwa wanda aka yi musu alkawarinsa, watau karbar ragamar mulki ko kuma tabbatar da abin da zai kusanta su da wannan, kamar juyin juya hali ta hanyar daukan makami. Kuma ‘Mai Tsayawa’ shi ne zai jagoranci wannan aikin.

A wata riwaya Hisham Ibn Salim wanda shi ma wani babba ne kuma sananne daga cikin shi’a, ya ambaci cewa Zurara ya ce da shi: “Ba zaka ga wani kan karagar shugabanci ba face Ja’afar.” Ya ce: Yayinda  Abu Abdillah ya yi wafati sai na zo na ce masa (Zurara): Kana tuna labarin da ka bani? Na ambata masa shi, ina mai tsoron kada ya yi musun cewa ya fada mini. Sai ya ce: “Wallahi ni ban fadi waccar maganar ba face dama nawa ra’ayin ne(watau dama ba ya ruwaito maganar Imam ba ne)”.

Daga  jumlar abin da ya gabata muna fahimtar cewa a ra’ayin babansa da na jama’a Imam Sadik (a.s) shi ne mai tabbatar da burin imamanci da shi’anci. Kuma silsilar imamanci ta riga ta yi tanadinsa domin tabbatarda kokarin Imam Sajjad da Imam Bakir(a.s) . Kamar dai shi ne ya wajaba a kansa ya dawo da ginin hukumar Alawiyya da tsari irin na tauhidi,watau ya wajaba ya aiwatar da wani sabon yunkurin musulunci. Imaman nan biyu da sauka gabata sun riga sun ci zango-zango masu wahala da kunci a kan wannan gwadabe, shi kuma sai ya ji da zangon karshe.  Kamar yanda muka ambata, yanayi ya daidaita ga Imam kuma ya yi amfani da wannan dama wajen yukurin gabatar da sakonsa mai girma.

Tun lokacin da ya karbi nauyin shugabaci har zuwa wafatinsa, Imam ya dauki shekara talatin da uku yana jihadi maras yankewa. Cikin wadannan shekarun yanayi ya kasance yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana hawa da kuma sauka;wani zubi ya dace da maslahar mazhabin Ahlulbaiti, wani zubin kuwa yanayin ya juya akasin hakan. Wani lokaci halin yana sa kyakkyawar fata, wani lokacin kuma matsin lamba yana tsanani, har sahabban Imam su zaci cewa dukkan buri ya tarwatse. A duk wadannan halaye Imam Sadik(a.s) yana rike da ragamar jagoranci kyam tare da azama da jajircewa. Yana keta fagen nan mai rudani, mai tattare da tsammani da kuma yanke kauna, ba ya damuwa da komai sai tafiyar da ke

  gaba yana wanzar da kokari da karfin gwiwa da imani wa mabiyansa domin kaiwa ga tsira.

A nan ya zama wajibi mu yi nuni da wani al’amari mai ban takaici wanda dukkan masu bincike kan rayuwar Imam Sadik(a.s) suke fuskanta .

Wannan kuwa shi ne halin rashin tabbas wanda ya lullube shekarun farkon imamanci Sadik(a.s) wadanda suka yi muni daidai da karshen zamanin Banu Umayya. A lokacin rayuwa ba ta san natsuwa ba tana kuma cike da aukuwar manya-manyan al’amura,muna iya fahimtar alamunsu cikin daruruwan riwayoyi. Sai dai malaman tarihi da hadisi basu kawo mana labarin wannan lokacin a jere tare da sajewa da daganta wannan bayani da wancan ba. Saboda haka ya zama dole ga mai bincike ya yi dogaro da kuma lura da al’amura da suke baiyana cikin abinda yake karantawa (kara’in), ya lura da kungiyoyi da ra’ayoyi a game na wancan zamani sannan ya kwatanta ko wace riwaya da bayanan da ya riga ya sani domin ya ga abin fahimtar(mafhumi) abinda riwayar ta kunsa da rabe-raben ta.

La’alla daya daga dalilan wannan rikitarwa shi ne kasancewa harakar Imam da mabiyansa an yi ta cikin sirri, domin shiri na siri wanda ya kafu bisa ingantattun ginshikai dole ne bayanan da suka dangance shi su wanzu cikin sirri da boyewa, kuma wajibi ne kada wanda yake waje da wannan shiri ya tsinkaye su. Wadannan bayanai ba su watsuwa sai bayan tabbatar harakar da kuma nasararta. Saboda haka ne muke samun cikakkun bayanai dalla-dalla kan sadarwa ta sirri a harakar Abbasiyawa domin harakarsu ta yi nasara.  Babu shakka da an kaddara wa harakar Ahlulbaiti kaiwa ga nasara da karbar ragamar mulki da a yau mun riski sirrin tsare-tsarenta masu fadi.

  Akwai wani dalilin daban wanda zai iya janyo wannan rashin baiyana dangane da harakar Ahlulbaiti, cewa murubuta tarihi, bisa al’ada suna rubuta abin da yake dadada wa sarakuna ne. Domin haka muke ganin bayanai filla-filla kan rayuwar halifofi da wasanninsu da hirarrakinsu da wuraren holewarsu amma bamu ganin bayanan kirki kan masu neman juyi da wadanda aka zalunta da wadanda aka murkushe. Domin samun irin wadannan bayanan mai bin diddigi na bukatar dogon bincike da kirkado da tsananin biyawa. Amma rayuwar halifofi bayani ne tanadadde, tsuntsu daga sama gasashshe, yana kawo yardarsu da tarin kyaututtuka.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next