Tafarki Zuwa Gadir Khum



Ubangiji Mahaliccinmu, kai kuma Shugabanmu

Ba a ga wani a cikinmu mai sabawa cikin wilaya ba

Sai ya ce tashi ya Ali hakika cewa ni na yarda

Da kai bayana Imami kuma mai shiryarwa

A nan ne ya yi addu’ar Allah ka taimaki wanda ya bi shi

ka kuma zama makiyi ga wanda ya zama makiyin Ali

Abubuwan Da Suka Faru A Tarihin Hijira

Abu Na Farko

Hijira ta kasance abin da ya ta’allaka da tarihin rayuwar dan Adam tun farkon bayyanar tarihi har zuwa yau. Haka nan kuma ba za ta gushe al’amari na zamantakewar dan Adam ba tana mai kunshe da abubuwa da suka zama mafitarsu ta doru a kanta ne. Idan abin ya zama gwagwarmaya da dauki-ba-dadi tsakanin zalunci, to abin yakan zama abu mai girma na tarihi, kuma farkon shafi na rayuwar wata al’umma ko dan Adam mai hijira.

Zalunci ya yi kamari a Makka har ya zama ba malumfasa, rayuwar mutanen da suka yi imani da sakon sama ta zama abu mai wahalar jurewa. Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana so ya gina rayuwa mafificiya ga mabiyansa. Hijira zuwa Habasha ta zama warwara ga wahalhalu na wani dan lokaci har zuwa lokacin da haduwar Akaba ta wakana.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 next