Tambayoyi da Amsoshi



A: Bai halatta ba Canza takalid daga A'alam zuwa ga wani mujtahidi saboda kawai zaton rashin dacewar tatawoyinsa da irin yanayin da ke kewaye da su, ko kuma dan kawai kasantuwar akwai wahala cikin aiki da wadannan fatawoyi.

MAS'ALOLI DABAN- DABAN KAN TAKLID

T34: Mene ne ma'anarjahilul mukassir?

A: Jahilul muRassir: Shi ne jahilin da ya san shi jahili ne, kuma ya san hanyoyin da zai iya bi wajen kawar da jahilcin anmma ya ki ya bi su.

T35: Wane ne kumajahilul kasir?

A: Al- Jahilul Raasir: Shi ne wanda bai fadaka da jahilcinsa ba, ko kuma bai san hanyar da zai bi wajen kawar da jahilcin nasa ba?

T36: Mene ne ma'anar ihtiyati na wajibi?

A: Ma'anarsa shi ne wajibi ne ayi aiki ko abar aikata wani aiki saboda ihtiyati (ko kuma a koma ga wani marja'i).

T37: Shin wannan lafazi ta "fihi ishkal" (akwai matsala a cikinsa) wanda ake kawo shi a cikin fatawoyi yana nufin haramci ne?

A: Ma'anarta tana banbanta gwargwadon yadda ta zo, idan har matsalar a wajen halacci ne to tana nuna haramci ne a fagen aiki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next