Tambayoyi da Amsoshi



A: Ba wata matsala wajen binne su cikin kasa, ko kuma mayar da su gari, to amma kona su akwai matsala, idan ana ganin konawa a matsayin walakantarwa ne to ba ya halatta, sai dai idan yin hakan ya zama lalura kana ba za'a iya yanke ayoyin kur'anin ko sunaye masu albarka ba.

TI06: Mene ne hukuncin yayyanke sunaye masu albarka da ayoyin kur'ani yayyenkewa ta yadda babu wasu haruffa guda biyu da suka hade ballantana su karantu? Kana shin caccanza yanayin rubuta su ta hanyar kara wasu haruffa a kansu, ko kuma shafe wasu haruffa yana wadatarwa wajen goge su da kuma faduwar hukuncinsu?

A: Yayyenkewa ba ya wadatarwa matukar dai bai haifar da shafe rubutun sunan Allah ko ayoyin kur'anin ba, kamar yadda canza yanayin shakalin rubutun ba ya wadatarwa wajen gusar da, wannan hukunci akan haruffan da aka zana su da nufin rubuta sunan Allah, Na'am bai yi nisa ba ace hukuncin yana iya faduwa bayan canza shakalin haruffan, ta hanyar ba shi hukuncin shafewa ko da yake ihtiyat shi ne a nisanci yin hakan.

HUKUNCE-HUKUNCEN WANKAN JANABA

T107: Shin ya halatta ga mai janaba ya yi salla da taimama kana da kuma najasar da ke jiki da tufafinsa idan lokaci ya yi kunci ko kuma ya jira har ya yi tsarki kana ya yi wanka sannan ya yi salla a matsayin ramako?

A: Idan har lokaci ba zai ba shi daman ya tsarkake jiki da tufafinsa ba, ko kuma ya canza tufafin ba, kana kuma ba zai iya salla tsirara ba saboda sanyi da makamancinsa, to sai ya yi salla a wannan hali cikin najasar amma tare da yin taimama wadda za ta zama a maimakon wankan janaba kuma ta wadatar kana ba wajibi ba ne ya rama ta.

T108: Shin isar da maniyyi zuwa ga mahaifa ba ta hanyar jima'i ba yana haifar da janaba?

A: janaba ba ta tabbatuwa da haka.

T109: Shin wajibi ne ga mata bayan binciken da ake musu a cikin jikinsu ta hanyar amfani da kayan ayyukan likitanci da su yi wankan janaba.

A: Ba wajibi ba ne su yi wanka matukar dai maniyyi bai fito musu ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next