Tambayoyi da Amsoshi



T85: Shin share ruwan alwala bayan idarwa makaruhi ne? Kana rashin sharewan mustahabi ne ?

A: Idan har an kebance wa wannan aiki wani kyalle na musamman, to babu wata matsala ga hakan.

T86: Shin irin launi da mata suke shafawa akan gashin kai da giransu don rina su yana bata alwala ko wanka?

A: Idan har ba shi da maikon da zai hana isar ruwa ga gashin, shi dai kawai launi ne, to ba ya bata alwala ko wanka.

T87: Shin ruwan biro yana daga cikin abubuwan da suke hana isar ruwa ga fata, ta yadda kasantuwarsa a hannu kan iya bata alwala?

A: Idan har yana hana isar ruwa ga fata to yana bata alwala, gane hakan kuwa yana hannun mukallafi ne.

T88: Idan danshin shafa kai ya hadu da danshin fuska, shin alwala ya kan baci.

A: Babu matsala ga hakan, to amma kasantuwan ihtyat yayin shafan kafa shi ne ayi shafan da sauran danshin alwala da ya rage a hannu. to lalle ne ayi Ihtiyat wajen kare isan hannu zuwa ga goshi yayin shafan kai, ta yadda ba zai hadu da danshin da ke fuska ba, don kada danshin hannu wanda za'a shafa kafa da shi ya hadu da danshi fuskar.

T89: Mene ne hukuncin ruwan da ake kokwantonsa cewa fitsari ne ko maniyyi wanda ya fito bayan mutum ya yi fitsari da kuma istibra'i kana kuma ya yi alwala?

A: A wannan yanayi wajibi ne a hacfa alwala da wanka don a sami yakini kan tsarki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next