Tambayoyi da Amsoshi



T14: Shin takiidin mujtahidi mamaci, ya dogara ne kan taklidin rayayyen mujtahidi ko kuma a'a?

A: Halaccin taklidin mamaci a farkon farawa, ko kuma ci gaba da takalidin mamaci duka ya ta'allaka ne da izinin rayayyen mujtahidi A'alam.

HANYOYIN TABBATAR DA IJTIHADI DA A’ALAMIYYA DA KUMA GANO FATAWA

T15: Shin ya wajaba a gare ni bayan na gano cancantar wani mujtahidi ta hanyar shaidar adilai guda biyu in sake tambayan wasu kan hakan?

A: Yana inganta a takaita ga shaidar adilai guda biyu daga cikin ma'abuta sani (Ahlul khibra) kan cancantar wani mujtahidi wanda ya cika sharuda, ba wajibi ba ne sai ya sake tambayar wasu jama'a.

T16: Yaya ake zaben marja'i da kuma karban fatawoyinsa?

A: Gano ijtihadi ko kuma A'alamiyyar marja'in Taklid dole ne ya zamanto ta hanyar gwani, ko kuma ta hanyar ilimi kan haka ko da kuwa ilimin ya samu ne ta hanyar yaduwar labarin cikin mutane ko kuma ta hanyar samun nitsuwa ko kuma ta hanyar ba da shaidar adilai biyu daga masana. Shi kuwa fatawar mujtahidi akan same ta ne ta hanyar ji daga gare shi, ko kuma daga fadin adilai biyu, kai ko da ma adali guda daya ne, ko kuma daga fadin wani amintacce wanda ake nitsuwa da maganarsa, ko kuma ta hanyar komawa ga risalarsa wacce ta kubuta daga kura-kurai.

T17: Na tambayi wasu malamai kan wane ne A'alam sai suka amsa min da cewa yin taklid wa wane (suka ambaci sunansa)yana wadatarwa, to shin yana halatta in dogara  ga  maganarsu  tattare  da  jahilcina  kan A'alamiyyarsa ko kuma zatona ga a alamiyyarsa ko, kuma ya halatta in dogara kan nitsuwa da nake da ita a kan cewa ba shi ba ne A'alam domin kasantuwan wasu mutane da su ma aka ba da irin wannan shaidar dangane da su, da kuma ire- iren wannan halaye?

A: Idan har dalili na sharia(shaidar adilai biyu) ya tabbata kan A'alamiyyar mujtahidin da ya cika sharudda, matukar dai ba a sami mai inkarin wannan shaidar ba, to ita wannan shaidar ta zama hujja ta shari'a wanda za a dogara a kan ta kana ba sharadi ba ne a ce sai an sami yakini ko nitsuwa a kan haka, saannan kuma babu bukatar a wannan hali a ce za a binciko wata shaidar da ta saba hakan.

AL-UDUL (CANZA TAKLIDI)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next