Tambayoyi da Amsoshi



T55: Yayin tsarkake tafin kafa an shardanta taku goma sha biyar, to shin wannan bayan gushewar najasar ne ko kuma ko da ainihin najasar tana nan? Sannan tafin kafa yana tsarkakuwa ne da taku goma sha biyar bayan gushewar ainihin najasar idan mutum ya yi tafiya da kafar?

A: Abin lura ba shi ne taku goma sha biyar ba, face dai abin da ke wadatarwa shi ne takun da a dalilinsa ainihin najasar za ta iya gushewa. Kana kuma idan da najasar ta gushe kafin ya yi tafiya, to yanzu sai ya  dan yi tafiya kadan shi kenan.

T56: Shin za'a iya daukar hanyoyin da aka sanya musu kwalta da dai makamancinsa a matsayin kasa mai tsarkakewa ta yadda za su iya tsarkake tafin kafa yayin tafiya a kansu?

A: Kasar da aka sanya mata kwalta da makancinta ba ta tsarkake cikin tafin kafa ko kuma abin da aka sanya wa tafin kafar kamar takalmi.

T57: Yaya za'a iya tsarkake tufafi masu najasa wadanda launinsu yake zuba a cikin ruwan yayin tarkake su?

A: Idan dai har zuban launin ba zai iya canza ruwan ya koma "mudaf' ba, to za'a iya tsarkake su ta hanyar zuba ruwa a kansu.

T58: Mutum ne ya zuba ruwa a langa dan wankan janaba, to yajin da yake wankan sai wani sashi na ruwan da ke zuba daga jikinsa ya kasance yana komawa cikin langar, to shin a wannan halin ruwan yana nan da tsarkinsa? Shin akwai wani abin da zai hana gama wankan da shi wannan ruwan?

A: Idan har ruwan da ke zuba cikin langa  din yana zuba ne daga sashin jikinsa wanda ke da tsarki to ruwan yana da tsarki kuma babu wani abin da zai hana gama wankan da shi.

HUKUNCE- HUKUNCEN SHIGA BAYAN GIDA

T59: Misali irin kabilun nan masu yawo daga guri zuwa guri kamar fulani idan ba su mallaki ruwan da za su yi tsarkin fitsari ba musamman a ranakun da suke kauran, shin tsarki da tsakuwa ko kuma itace yana wadatarwa?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next