Tambayoyi da Amsoshi



A: Abin da ba ruwa ba ba ya tsarkaka gurin fitsari, to idan har bai samu daman tsarkake shi da ruwan ba, to sallarsa ta inganta.

T60: Mene ne hukuncin tsarkake mafitar fitsari da bayan gida da ruwa kadan ma'ul kalil.

A: Wanke mafitar fitsari sau daya yana wadatarwa, amma mafitar bayan gida wajibi ne a wanke shi har sai ainin najasar da alamunsa ya gushe.

T61: A bisa al'ada wajibi ne ga mai salla bayan gama fitsari ya yi istibra'i to amma ni ina da wani ciwo a al'aura ta, yayin da nake istibra'i jini ya kan fito min a dalilin mammatse shi da nake yi kana ya hadu da ruwan da nake amfani da shi wajen tsarkin sannan ya najasta min jiki da tufa, kana idan har ban yi istibra'i ba to ina sa tsammanin warkewan ciwon, kuma abu ne sananne cewa ciwon zai ci gaba da wanzuwa idan na ci gaba da istibra'i saboda mammatse al’auran da nake yi, dan haka nake so ka min bayani shin zan yi istibra'i ko kuma a'a?

A: Shi dai istibra'i ba wajibi ba ne, face ma dai idan har zai haifar da cutarwa to ba ya halatta a yi shi Na'am idan har ba'a yi istibra'i ba bayan gama fitsari sai wani danshi mai rikitarwa ya fito to ana daukansa a matsayin fitsari ne.

T62: A wasu lokuta wani danshi (ruwa) mai kama da fitsari ya kan fito ma mutum ba tare da son sa ba bayan fitsari da kuma istibra'i, to shin wannan danshin najasa ne ko kuma yana da tsarki? Kana idan mutum ya fahimci hakan bayan wani lokaci, to mene ne hukuncin sallolin da ya riga ya yi sannan shin wajibi ne a nan gaba ya binciki fitar wannan danshi da ke fita ba tare da zabinsa ba?

A: Idan wani danshi ya fito bayan istibra'i kana aka yi shakkan kasantuwarsa fitsari to bai da hukuncin fitsari, yana da tsarki, ba wajibi ba ne a yi wani bincike.

T63: Da za ka yi mana cikakken bayani kan nau'oin ruwa da suke fitowa daga jikin mutum.

A: Ruwan da a wasu lokuta yake fitowa bayan maniyyi ana kiransa da' wazi", kana ruwan da ke fitowa a wasu lokuta bayan fitsari ana kiransa da "wadi", sannan ruwan da ke fitowa a wasu lokuta bayan wasanni tsakanin ma'aurata biyu ana kiransa da "mazi" dukkan wadannan ruwa masu tsarki ne, ba sa warware tsarki.

T65: Aiki a wasu kamfanoni da kuma mu'assasosi: ya ta'allaka da gudanar da wasu bincike kan lafiyar mutum wanda hakan yakan kai ga bude al'aura wani sa'i, to shin hakan ya halatta idan akwai bukatuwa ga aikin?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next