Tambayoyi da Amsoshi



A: Ba kawai ya kebanta da littafin al-kur'ani ba ne, a'a ya hada da kalmomi da ayoyin al-kur'ani ko da kuwa a wani littafi na daban ne, ko cikin jarida, ko mujalla, ko allo ko kuma rubutu a jikin garu da dai sauransu .

T96: A jikin wasu kwanuka da farantai da iyalanmu suke cin abinci an rubuta wasu ayoyin al-kur'ani kamar atul kursiyyi, niyyarsu na yin hakan kuwa shi ne neman alheri da kuma albarka, to shin akwai wata matsala cikin    yin hakan?     

A: Babu matsala ga hakan, sai dai wajibi ne a kiyaye kada a taba ayoyin kur'ani ba tare da alwala.ba.

T97: Shin wajibi ne ga mutanen da suke rubuta sunayen Allah ko ayoyin kur'ani ko sunayen ma'asumai (a.s) ta hanyar injunan rubutu su kasance cikin alwala yayin rubutun?

A: Ba sharadi ba ne a kasance cikin alwala sai dai taba rubutun ba tare da alwala ba ba ya halatta.

T98: Mene ne hukuncin amfani da kan sarki da ake amfani da shi wajen aika wasiku (stamp) wadanda aka rubuta musu ayoyin kur'ani, kana mene ne hukuncin buga sunayen Allah da buga ayoyin alkur'ani ko kuma buga take da kirarin wasu cibiyoyi wanda aka hada da alkur’ani a cikin jarida da mujalloli da suke yadawa kowace rana?

A: Ba matsala wajen bugawa da kuma yada ayoyin kur'ani da sunayen Allah da makamancinsu, sai dai wajibi ne ga wanda suka isa ga hannunsa ya kiyaye hukunce-hukuncen shari'a na rashin wulakanta su da kuma najasta su, da kuma taba su ba tare da alwala ba.

T99: Shin ya halatta ga masu sai da kayayyaki da su kunshe abin sayarwarsu da jaridun da suke da sunan Allah ? kana shin ya halatta a taba su ba tare da alwala ba?

A: Amfani da wadannan jaridu wajen kunshe abin sayarwa babu matsala a cikinsa idan har ba ganin hakan wulakanta sunayen Allah da ayoyin kur'ani da kuma sunayen imamai (as) da aka rubuta a jiki ne, to amma dai ba ya halatta ga mara alwala ya taba su alhali yana sane da shi.

T100: Mene ne hukuncin rubuta sunayen annabawa da kuma ayoyin al-kur'ani a cikin jarida Tare da yiyuwan kona su ko kuma fadawansu kasan kafa?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next