Tambayoyi da Amsoshi



A: Hukunce- hukuncen jagoranci da suka fito daga wajen "waliyi amril muslimin" da ya rasu in dai har ba na takaitaccen lokaci ba ne, to tana nan daram, sai dai idan sabon jagoran yana ganin akwai wata maslaha wajen shafe su, to yana da daman shafe su.

T46: Shin wajibi ne ga fakihin da yake zaune a jamhuriyar musulunci  ta Iran idan har bai  yarda da "wilayatul fakih"mudlaka ba,da ya yi biyayya ga umarnin waliyul fakih ? to idan ya saba wa umarnin waliyul fakih shin za'a iya daukansa fasiki?sannan idan wani fakihi ya kasance ya yarda da "wilayatui fakih" mudlaka, to amma yana ganin shi ya dace da wannan matsayi, to shin idan ya saba wa umarnin jagora da ke jagoranci ana iya daukansa a matasyin fasiki?

A: Wajibi ne ga kowane mukallaf, ko da kuwa mujtahidi ne, da ya yi biyayya ga hukunce-hukuncen jagoranci(hukuma) na waliy amril muslimin, ba ya halatta ga wani ya saba wa jagoran da yake jagoranci saboda da'awar cewa shi ya fi shi dacewa, hakan kuwa wajibi ne idan har shi jagoran da yake jagorancin ya hau wannan matsayin ne ta hanya da ta dace da dokokin da aka tsara domin haka, to amma in ba ta wannan yanayin ba, to al’amarin ya bambanta.

T47: Shin mujtahidin da ya cika sharudda a zamanin Buya (gaiba) yana da ikon zartar da haddi?

A: Wajibi ne a gudanar da haddi a lokacin gaiba,ikon hakan kuwa yana hannun waliyi amril muslimin neKawai.

BABIN TSARKI

HUKUNCE-HUKUNCEN RUWA

T48: Idan sashin kasa na ruwa mara yawa (ai'maul kalil) wanda yake gangarowa daga sama ba da karfi ba ya shafi najasa, to shin sashin samansa yana nan da tsarki ko kuwa?

A: Sashin sama na ruwan da yake gangarowa yana da tsarki idan dai har gangarowar nasa ta kasance ta yadda za'a iya kiranta gangarowa ce daga sama zuwa kasa.

T49: Shin wajibi ne bay an wanke tufafi mai najasa da ruwa mai gudu ko kuma ruwan kur a matse shi a wajen ruwan kafin ya tsarkaka ko kuma yana ma iya tsarkakuwa idan aka matse shi a cikin ruwan?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next