Tambayoyi da Amsoshi



A: Ba ya halatta ga mutum ya bude al'aura gaba ga wani mutum ko da kuwa aikin da za a ba shi ya ta’allaka da hakan ne sai dai idan barin aikin zai sa shi cikin halin kaka nikai, kana kuma ya zama dole ne ya yi hakan.

HUKUNCE-HUKUNCEN ALWALA

T66: Akwai wani mutum da ya sanya wa kansa gashin,kari, idan har ya cire zai shiga cikin kunci, to shin ya halatta gare shi ya yi shafa akan wannan gashi (yayin alwala).

A: Ba ya halatta a yi shafa a kan gashin kari, face ma dai wajibi ne a kawar da shi dan shafa kai sai dai idan a kawar da shi  din akwai wahalan gaske da ya saba wa al'ada.

T67: Wani mutum yana cewa: Yayin alwala a zuba ruwa a fuska sau biyu kawai amma sau, uku yana Bata alwala, shin hakan gaskiya ne?

A: Zuba ruwa sau biyu ko fiye babu matsala a cikinsa, amma wanke fuska ko hannaye sama da sau biyu ba ya halatta.

T68: Shin za'a iya kirga man da a bisa dabi' ar  jikin mutum ya kan fito a kan gashin kan mutum ko fatansa har a kira shi a matsayin hajib(abin da ke hana isar ruwa ga fata).

A: Ba'a kirga shi a matsayin hajib sai idan ya kai yanayin da shi kansa mukallafi yake ganin sa a matsayin abin da zai hana isar ruwa zuwa ga fatar jiki ko kuma gashi.

T69: Mene ne idon sawu (al-ka'ab) wanda shi ne karshen wajen shafa yayin shafan Rafa?

A: A bisa mashhurin magana shi ne wurin da ya dan taso sama na kafar mutum wanda ake kira da tudun saman kafa, to amma kada a bar ihtiyat wajen isar da shafan har zuwa mahadan sawu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next