Tambayoyi da Amsoshi



T149: Mene ne hukuncin tufafin da ake ba da su ga masu wanki dan wankewa kasantuwa sauran wasu mutanen da ba musulmai ba su ma suna kawo wankin kayayyakinsu tattare da cewa su masu wankin suna amfani da wasu magunguna wajen wankin?

A: Tufafin da ake ba wa masu wanki idan har ba daman can suna da najasa ba ne to masu tsarki ne, haduwar tufafi da tufafin mabiya sauran addinai na daga cikin Ahlul-kitab ba ya najastar da su.

T150: Shin ruwan da ke zuba akan titi ta hanyar motocin diban shara idan ya fantsamu a jikin mutum, shin wannan ruwa ana hukunta shi da abu ne mat tsarki ko kuma mai najasa?

A: Abu ne mai tsarki sai dai idan mutum ya samu yakini kan cewa ruwan ya najastu ta hanyar haduwa da najasa.

Tl 51: Shin ruwan da ke taruwa a cikin' yan ramukan da suke kan tituna mai tsarki ne ko kuma najasa ne?

A: Wannan ruwa mai tsarki ne

T152: Mutum ne ya ke sai da abinci kana kuma yana amfani da hannunsa da ke da jika wajen hakan tattare da cewa ba'a san shi mabiyin wani addini ba ne, to shin wajibi ne a tambaye shi addininsa ko kuma ana iya gudanar masa da hukuncin tsarki (wato ko wani abu mai tsarki ne har sai in najastuwansa ya bayyana)? Tare da cewa shi ba daga garin musulmai ya ke ba.

A: Tambaya kan addininsa ba wajibi ba ne, ana iya gudanar da hukuncin tsarki gare shi da kuma abin da ya taba da jikinsa da ke da jika.

ABU MAI SA MAYE DA MAKAMANCINSA

T153: A wannan zamani namu ana amfani da alkwan "alkohol"  wajen  yin  da  yawa  daga  magunguna (musamman magungunan da ake sha) da kuma turare, shin ya halatta ga mutumin da ya san hakan ko kuma wanda ma bai sani ba da ya sayar ko ya saya ko kuma ya yi amfani da wadannan abubuwa?

A: "Alkohol" din da ba'a tabbatar da kasantuwarsa ruwa ba ne tun asali to shi yana da tsarki ko da kuwa yana sa maye, babu wata matsala wajen amfani da shi wajen magani da sauransu kamar yadda babu laifi wajen salla da tufafin da wannan alkwan "akohol" ya taba.

T154: Mene ne ake lura da shi wajen najastuwan "alkohol"? Kana wadanne hanyoyi ne ake bi wajen tabbatar da abin sha yana sa maye?

A: Abin da ake lura da shi ya kasance yana sa maye kana kuma ya kasance asalinsa ruwa ne. Sannan hanyar da ake bi ita ce ta hanyar ba da labarin wadanda suka san kan al'amarin idan har shi mukallafi bai da yakini a kan haka.

T155: Mene ne hukuncin shan lemunan kwalban da ake sayarwa a kasuwa (kamar su Coca- Cola, pepsi.....) tattare da akan ce ainihin abubuwa da ake yin su da su daga waje ake shigowa da su, kana kuma akwai yiyuwan cewa sun kunshi "alkohol"?

A: Masu tsarki ne kuma sun halatta a sha, sai dai idan shi mukallafi yana da yakinin cewa sun kunshi "alkohol" mai sa maye wanda asalinsa ruwa ne.

TI56: Yayin sayen kayayyakin abinci (musamman na gwangwani) shin wajibi ne a nemi sanin cewa sun kunshi "alkohol" ko kuma sun taba hannun wanda ya yi su ko kuma ba wajibi ba ne?

A: Tambaya ko bincike kan hakan ba wajibi ba ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33